Kotu ta ƙi aminta da buƙatar dakatar da yunƙurin tsige Mataimakin Gwamnan Kano
[ad_1]
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano, ta ƙi amincewa da buƙatar da Mataimakin Gwamnan Jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya gabatar na dakatar da shirin tsige shi.
Gwarzo, ta hannun lauyansa Umar Danbaito, ya roƙi kotu da ta bayar da umarni na wucin gadi domin hana Majalisar Dokokin Jihar Kano ci gaba da shirin tsige shi.
Sai dai alƙalin kotun, Mai shari’a S. M. Shaibu, ya ce bai cika sharuɗan da ake buƙata ba domin ba da irin wannan umarni.
Alƙalin ya kuma umarci Gwarzo da ya miƙa takardun kotu ga waɗanda ake ƙara domin su ba da amsa, sannan ya ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Afrilu, 2026.
Wannan na zuwa ne bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta fara shirye-shiryen tsige shi bisa zargin almundahanar kuɗi da kuma amfani da ofishinsa ba daidai ba, inda aka ba shi wa’adin makonni biyu ya kare kansa.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan majalisa 38 na jam’iyyar APC da kuma ’yan majalisa biyu na NNPP ne suka goyi bayan yunƙurin.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini, mai wakiltar Dala ne, ya gabatar da ƙudirin.
’Yan majalisar sun ce matakin ya yi daidai da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya bayyana yadda ake tsige mataimakin gwamna.
Sun zargi Gwarzo da karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba daga ƙananan hukumomi 44 na jihar tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Janairun 2024.
A cewarsu, yana karɓar Naira miliyan 1.5 a kowane wata daga kowace ƙaramar hukuma, wanda ya kai kimanin Naira miliyan 66 a wata, wanda kuma adadin ya kai Naira miliyan 462 cikin watanni bakwai.
Sun kuma yi zargin cewa tsakanin Fabrairu zuwa Yulin 2024, ya sake karɓar Naira miliyan 726, inda ya ce za a yi wasu ayyuka a ƙananan hukumomin.
Haka kuma, sun zarge shi da amfani da muƙaminsa ba daidai ba, inda suka ce ya taimaka wajen fitar da Naira miliyan 440 daga ƙananan hukumomin zuwa wani kamfani mai zaman kansa, Novomed Pharmaceuticals Limited, ba bisa ƙa’idojin fitar da kuɗi ba.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Mataimakin Gwamnan bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link