’Yan Bindiga Sun Sace Mutane Da Dama A Wani Sabon Hari A Katsina

[ad_1]

’Yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare wasu yankuna a Jihar Katsina a daren ranar Litinin, inda suka sace mutane da dama.

Maharan sun ɗauki tsawon lokaci suna sharafinsu.

  • Chelsea Ta Naɗa Liam Rosenior A Matsayin Sabon Kocinta
  • Guterres Ya Zargi Amurka Da Take Dokar Ƙasa Da Ƙasa A Venezuela

’Yan bindigar sun kai farmaki Unguwar Alhaji Barau, Gidan Dan Mai-gizo da Gidan Hazo, duk a Ƙaramar Hukumar Malumfashi.

Sun yi awon gaba da mutane da yawa, amma har yanzu ba a san adadin da suka sace ba.

Mazauna yankin sun ce harin ya jefa mutane cikin tsoro da firgici, inda da dama suka tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu.

Har yanzu wasu magidantan na neman ’yan uwansu da aka sace.

’Yansanda sun ce ba su samu cikakken bayani kan lamarin ba, amma sun yi alƙawarin gudanar da bincike da yin ƙarin bayani.

Ƙaramar Hukumar Malumfashi na daga cikin yankunan da ke fuskantar yawaitar hare-haren ’yan bindiga a Jihar Katsina, duk da ƙoƙarin samar da zaman lafiya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *