Ba ma yin barci saboda hare-haren ’yan bindiga — Hakimin Gundala

[ad_1]



Al’ummar garin Gundale da ke kan iyakar Jihar Taraba a kudancin Jihar Gombe, a Ƙaramar Hukumar Shongom, na rayuwa cikin fargaba da tashin hankali saboda yawaitar hare-hare da satar mutane.

Hakimin Gundale, Alhaji Aliyu Ibrahim, ya ce mazauna garin ba sa iya barci saboda yadda ’yan bindiga ke sace mutanen garin.

“Gaskiya ba ma iya barci da ido biyu a rufe. ’Yan bindiga na shigowa garinmu ana kallo za su ɗauki mutane. A makon jiya kaɗai an sace mutum bakwai,” in ji hakimin.

Hakimin ya ce duk da ƙoƙarin da ’yan banga da mafarauta ke yi matsalar ta fi ƙarfinsu, ganin cewa garin yana kusa da duwatsu kuma yana kan iyaka da Jihar Taraba, inda masu laifi ke amfani da dazuka wajen tserewa da waɗanda suka sace.

“Masu hali da ’yan kasuwa da dama sun daina kwana a Gundale saboda tsoron kada a sace su. kowane lokaci ’yan bindiga kan shigo gari suna farautar mutane,” in ji Alhaji Aliyu.

Hakimin ya roƙi gwamnati da ta taimaka musu ta hanyar kafa sansanin sojoji ko jami’an tsaro a yankin, tare da haɗin gwiwar mafarauta domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wasu mazauna garin da suka zanta da Aminiya, su sun bayyana cewa rayuwarsu na cikin hatsari, saboda yada ’yan bindiga ke shiga garin a kowane lokaci.

“Muna roƙon gwamnati da kada ta manta da mu. Mu ma ’yan ƙasa ne kamar kowa, ya kamata a kare rayuwarmu da dukiyoyinmu,” in ji wasu daga cikin mazauna garin.

Wani maharbi a Gombe da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayar da shawarar samar da sansanin mafarauta tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro.

Ya kuma nemi a ba su kayan aiki da babura don shiga daji, ganin cewa yankin akwai duwatsu.

“Rashin tsaro a Gundale ya kai matakin da ba a wuce sati ba tare da an kai hari ko an sace mutum ba. Wannan lamarin yana hana mutane yin noma, kasuwanci da zirga-zirga.

“Haka kuma matafiya da ke shigowa Jihar Taraba na fuskantar barazana a hanyoyin yankin,” in ji maharbin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *