Ya kamata a dakakar da hadimin Gwamnan Kano — Ƙungiyoyi

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kano ta yi shiru yayin da wasu ƙungiyoyin farar hula suka buƙaci ta dakatar da manyan jami’abta da ake zargi da almundahana ta biliyoyin naira tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Wani rahoto na kafar yaɗa labarai ta Daily Nigerian ya bayyana cewa hukumomin ICPC da EFCC masu ya ki da almundahana sun gano badaƙalar Naira biliyan 6.5 da ake zargin Abdullahi Ibrahim Rogo, Darakta Janar na Al’amuran Kula da Baƙi a Fadar Gwamnatin Kano.

Takardun da kafar ta ambato cewa ta samu suna zargin almundahanar ta faru ne tsakanin watan Nuwambar 2023 da Fabrairun 2025 ta hanyar kwangilolin bogi da sunan kamfanonin H&M Construction Nigeria Ltd, A.Y. Maikifi Petroleum da Ammas Oil & Gas Ltd.

Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin jihar ya ci tura, yayin da Kwamishinan Watsa Labarai, Ibrahim Wayya da Sakataran Gwamna ba su ɗauki kiran waya ba, kuma Darakta Janar na Watsa Labarai na Gwamnan, Sunusi Bature ya yi bukaguro zuwa ƙasar waje.

Wannan dambarwar na zuwa ne bayan rahoton jaridar Nigerian Tribune a watan Yuli 2025, wanda ya bayyana cewa ICPC ta kammala bincike kan badaƙalar Naira biliyan 1.02 da ake zargin jami’an Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC).

A wata sanarwa da wasu ƙungiyoyin fararen hula 20 suka sa hannu, sun yi gargaɗi cewa zarge-zargen na iya ɓata amincewar jama’a da gwamnati, tare da sare gwiwar masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma durƙushewar da ci-gaban jihar.

“Wannan ba ƙaramin lamari ba ne. Ya nuna tsarin almundahana ta hanyar amfani da muƙaman gwamnati don amfanin kai,” in ji ƙungiyoyin.

Sun kuma buƙaci a dakatar da duk jami’an da ake zargi tare da gudanar da bincike mai zaman kansa kan dukkanin ma’aikatun gwamnati.

Haka kuma sun buƙaci Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ƙarfafa aikin sa ido tare da kafa dokar kare waɗanda ke fallasa rashawa.

“Zaɓi yana a hannunmu: ko mu yaƙi rashawa mu dawo da martabar shugabanci ko kuma mu bari ta ƙara zurfi har ta kai ga rugujewar cibiyoyinmu da makomar ’ya’yanmu,” in ji sanarwar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *