Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN
[ad_1]
Ɗalibai 50 da aka sace a Makarantar St. Mary’s da ke garin Papiri, a Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, sun tsere daga hannun ’yan bindiga.
’Yan bindigar da suka sace su, sun kai hari makarantar da safiyar ranar Juma’a.
Maharan sun harbe mai gadin makarantar sannan suka sace ɗalibai sama da 200 da ma’aikatan makaranta 13, ciki har da malamai.
A farko, Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Jihar Neja, Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne mamallakin makarantar, ya ce ɗalibai 215 tare da ma’aikata 12 aka sace.
Sai dai a ranar Asabar, ya ce har yanzu ba inda ɗalibai 88 suke ba.
Amma a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Daniel Atori, ya fitar a madadinsa ranar Lahadi, Fasto Yohanna ya ce ɗalibai 50 sun tsere a ranar Asabar kuma sun koma gidajensu.
Sanarwar ta ce: “A ranar Lahadi, 23 ga watan Nuwamba 2025, mun samu labari mai daɗi cewa yara 50 sun tsere kuma sun koma wajen iyayensu.”
Rabaran Yohanna, ya bayyana cewa makarantar na da ɗaliban kwana da na jeka ka dawo, sashen firamare na da dalibai 430; inda sashen kwana ke da ɗalibai 377, na jeka ka dawo na da 53.
“A halin yanzu, ban da yara 50 da suka tsere, muna da yara 141 waɗanda ba a sace ba. Yanzu haka, yara 236 da ƙananan yara uku na ma’aikata, ɗalibai 14 na sakandare, da ma’aikata 12 na hannun maharan.”
Rahotanni sun nuna cewar hukumomin tsaro na ƙoƙarin ceto sauran da ke hannun ’yan bindiga.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link