Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Ta Gayyaci Shugabar Jam’iyyar Kuomintang Ta Ziyarci Babban Yankin Kasar

[ad_1]

Kwamitin kolin JKS da Xi Jinping, sakatare-janar na kwamitin, sun gayyaci Cheng Li-wun, shugabar jam’iyyar Kuomintang ta kasar Sin, ta ziyarci babban yankin kasar, daga rana 7 zuwa 12 ga watan Afrilu.

Cheng Li-wun, shugabar jam’iyyar Kuomintang ta Sin, ta bayyana godiya tare da amincewa da gayyatar da aka yi mata ta ziyartar babban yankin kasar Sin a watan Afrilu. Ta kuma bayyana fatan jam’iyyun biyu za su hada hannu wajen samar da ci gaba cikin lumana tsakanin yankunan kasar Sin da kara musaya da hadin gwiwa, da kuma bayar da gudunmawa ga tabbatuwar zaman lafiya a Mashigin Taiwan da kyautata rayuwar al’umma. (Fa’iza Mustapha)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *