Trump ya yi barazanar tarwatsa cibiyar makamashin Iran duk da tashin farashin man fetur
[ad_1]
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rusa muhimman cibiyoyin makamashin Iran, ciki har da tsibirin Kharg, muddin Tehran ba ta amince da yarjejeniyar sulhu cikin gaggawa ba, lamarin da ke ƙara tayar da haddasa fargaba a kasuwannin makamashi da na kuɗi a duniya.
Trump ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin.
A cewarsa, Amurka za ta lalata tashoshin lantarki, rijiyoyin mai da sauran muhimman cibiyoyin makamashi muddin Iran ba ta buɗe Mashigar Hormuz ba tare da ɓata lokaci ba.
Barazanar na zuwa ne a daidai lokacin da farashin mai ya riga ya tashi matuƙa, inda ɗanyen man nau’in Brent ya ƙaru da kusan kashi 60 cikin ɗari a wannan watan, yayin da man WTI na Amurka ya haura sama da rabin darajarsa.
Masana sun yi gargaɗin cewa muddin rikicin Gabas ta Tsakiya ya a ci gaba tsanani musamman idan Amurka ta kai farmakin ƙasa ko Iran ta ƙara kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi, na iya sa farashin mai ya kai dala $200 kan kowanne ganga.
A nata ɓangaren, Iran ta yi barazanar kai hari kan cibiyoyin makamashi da na samar da ruwa a ƙasashen Larabawa da suka yi wa sojojin Amurka sansani, ciki har da Haɗɗaɗiyar Daular Larabawa, Qatar, Saudiya da kuma Oman.
Masana dokokin ƙasa da ƙasa sun kuma yi gargaɗin cewa duk wani hari kan cibiyoyin lantarki da na ruwa na fararen hula na iya zama laifi a ƙarƙashin dokokin yaƙi na duniya.
A fannin diflomasiyya kuwa, Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya roƙi Trump da ya nemo hanyar kawo ƙarshen rikicin, yana mai cewa yana da ikon dakatar da yaƙin.
A gefe guda, rikicin na ci gaba da ƙamari, inda Isra’ila ta ce ta kai hare-hare a Tehran, yayin da aka kuma samu gobara a wata matatar mai a birnin Haifa.
Duk da haka, ana ci gaba da ƙoƙarin sasanta rikicin, inda ƙasashe da dama ciki har da Pakistan ke taka rawa wajen shiga tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen yaƙin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link