Duniya Ta Ga Damammaki Daga Fasahohi Da Kimiya Na Zamani Na Sin
[ad_1]
Taron dandalin Zhongguancun da aka kammala ba da dadewa ba, ya baje kolin sakamakon kimiyya da fasaha na zamani fiye da 560 a cikin dakin baje koli mai fadin murabba’in mita dubu 10, wanda ya nuna karfin kirkire-kirkire na gaske. Baki mahalarta taron daga ketare, sun ga damammakin da Sin ke da su, ta hanyar gwada wadannan fasahohi masu kayatarwa. Tabarau mai fasahar AR, mutum-mutumin inji masu siffar bil Adam, mutum-mutumi na dabbobin gida da dai sauran abubuwa masu alaka, na daga cikin kayayyakin da aka baje yayin bikin, inda duniya ta ga damammaki daga wajensu.
Shugaban ofishin kula da harkokin yankuna da dama na gabashin Asiya na hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO) Shahbaz Khan ya bayyana cewa, shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, shiri ne mai ban mamaki. Ya ce shirin ya jaddada wajibcin raya fasaha da kimiyya, wanda zai kara karfin samar da kayayyaki da hidimomi a fannonin samar da sabbin kayayyaki ta hanyar amfani da AI ko mutum-mutumin inji na masana’antu, haka kuma zai samar da sabbin damammaki na kirkire-kirkire a fannonin motoci masu amfani da lantarki da sadarwa da sauransu.
Shi kuwa shugaban kwamitin bayar da shawara na cibiyar kirkire-kirkire da ci gaba mai dorewa ta hukumar UNESCO Hans d’Orville ya nuna cewa, Sin tana kokarin zama babbar kasa a fagen AI, kuma fa’idar Sin a yanzu ita ce, ta riga ta mallaki kayayyakin aikin AI masu ingantacciyar kwarewa, wadanda za su iya samar da kayayyaki masu inganci, sannan za su shiga kasuwannin duniya.(Amina Xu)
[ad_2]
Source link