Najeriya da Turkiyya sun ƙulla yarjejeniya kan yaƙi da ta’addanci

[ad_1]



Najeriya da Turkiyya sun sanya hannu kan sabbin yarjejeniyoyin tsaro domin yaƙi da ta’addanci.

An sanya hannu kan yarjejeniyoyin har guda tara ne a Ankara, babban birnin Turkiyya tare da Shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan yayin ziyarar da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yake yi a kasar.

Yarjejeniyoyin sun shafi haɗin gwiwa a fannoni kamar manufofin ’yan gudun hijira, yaɗa labarai, ilimin gaba da sakandare, cinikayyar halal, harkar soja, da diflomasiyya.

Haka kuma, kasashen sun amince su kafa wani Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci (JETCO) a tsakanin su.

Erdogan ya yi alkawarin tallafa wa Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci, inda ya ce Turkiyya za ta san wa ƙasar ƙwarewarta a horon soja da leƙen asiri.

Tinubu yana ziyarar aiki daga 26 zuwa 28 ga watan Janairu, inda ake sa ran tattaunawa kan kasuwanci, saka hannun jari, makamashi, ilimi da masana’antar tsaro.

Ƙasashen biyu sun sanya yarjejeniyar tsaro mai suna “yarjejeniyar haɗin gwiwa kan sojoji“ wadda ta ba Najeriya damar sayen kayan aikin soja na Turkiyya kamar jirage marasa matuka na Bayraktar TB2, jiragen T129 ATAK masu saukar ungulu, da kuma jiragen sintiri a kan ruwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *