Kamfanin Matatar Man Fetur Na Dangote Ya Sake Jaddada Tabbatar Da Daidaitacciyar Kasuwa
Kamfanin Matatar Man Fetur na Dangote ya sake jaddada alƙawarin da ya ɗauka na tabbatar da daidaito a farashi da kuma samar da ingantaccen Man Fetur (PMS) a duk faɗin ƙasar.
A lokacin bukukuwan Kirsimeti da na karshen shekara da suka gabata, Matatar Dangote ta aiwatar da wani shiri na tallafi, inda ta rage farashin man fetur ga ‘yan Nijeriya.
Duk da rage farashin, gidajen mai da yawa sun kasa rage farashin a famfon sayar da man fetur din, wanda hakan ya hana ‘yan Nijeriya samun fa’idodin rage farashin.
Da aka kammala lokacin bukukuwan, an daidaita farashin PMS zuwa matakan da suka dace don tallafawa dorewar kasuwa da araha na dogon lokaci. A ƙarƙashin farashin da ake da shi a yanzu, ana sayar da Fetur akan N839 kowace lita a gidan mai na MRS
Babban jami’in gudanarwa na matatar mai ta Dangote, David Bird, ya bayyana cewa matatar tana ci gaba da samar wa kasuwar cikin gida kimanin lita miliyan 50 na PMS a kowace rana.