Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa

[ad_1]



Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta.

Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen.

“Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:00 na rana, kuma jami’anmu daga sashen Yalwawa sun garzaya wurin. Da suka isa, sun tarar da gawar matar a rataye,” in ji shi.

Shi’isu ya ƙara da cewa an kai gawar zuwa Asibitin Gwamnati na Dutse, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

Duk da cewa ba a samu cikakken bayani kan lamarin ba, majiyoyi sun ce marigayiyar ta dade tana fama da matsalar kwakwalwa kafin rasuwarta.

Da yake tsokaci a kan lamarin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar ta Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai kira ga al’umma da su ƙara wayar da kai kan batun lafiyar kwakwalwa.

“Muna roƙon iyalai da maƙwabta da su nuna kulawa ga duk wanda ke nuna alamun damuwa ko canjin hali. Neman taimakon likita da na ƙwararru da wuri na iya ceton rayuka,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma buƙaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani hali da ba a saba gani ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko cibiyar lafiya domin a samu matakin gaggawa.

Marigayiya Adama ta rasu ta bar mijinta da ’ya’ya hudu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *