Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Firaministan Birtaniya

[ad_1]

Da safiyar yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan Birtaniya Keir Starmer, a babban dakin taruwar jama’ar kasar Sin dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin tattaunawarsu bangarorin biyu sun amince cewa, ya zama wajibi Sin da Birtaniya su bunkasa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni kuma mai dorewa tsakaninsu.

Xi ya nuna cewa, a halin yanzu ana fuskantar yanayin kasa da kasa mai sarkakiya da sauye-sauye, kuma Sin da Birtaniya a matsayinsu na mambobin dindindin a kwamitin sulhun MDD, kana manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, suna bukatar karfafa tattaunawa, da hadin gwiwa, ba ma don kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya kadai ba, har ma da burin inganta tattalin arzikin kasashen biyu da rayuwar jama’arsu.

Shugaba Xi ya ce bangaren Sin yana fatan ci gaba da hadin gwiwa da bangaren Birtaniya, ta yadda za su mutunta tarihi, da yin watsi da sabanin ra’ayi, da mutunta juna, domin sarrafa boyayyen karfin hadin gwiwarsu zuwa ainihin matakan ci gaba, ta yadda za a bude sabon babi ga bunkasuwar dangantakar Sin da Birtaniya da hadin gwiwarsu, wanda zai yi amfani ga al’ummomin kasashen biyu, kuma ya amfani duniya baki daya.

A nasa bangare, Starmer ya mika gaisuwar Sarki Charles na III ga shugaba Xi. Ya kuma bayyana cewa, yana farin cikin zama firaministan Birtaniya na farko da ya ziyarci Sin tun bayan shekarar 2018. A wannan ziyarar, ya jagoranci fiye da wakilai 60 masu muhimmanci a fannin kasuwanci, da al’adu na Birtaniya domin ziyartar kasar Sin, matakin da ya habaka hadin gwiwar Birtaniya da Sin, da kuma ingiza azamar bangaren Birtaniya na zurfafawa, da fadada hadin gwiwarta da Sin.

Firaminista Starmer, ya kara da cewa Birtaniya da Sin manyan kasashe ne masu karfin tattalin arziki a duniya, kuma mambobin dindindin na kwamitin sulhun MDD. Don haka yana da mahimmanci matuka ga bangaren Birtaniya, ya kulla dangantakar hadin gwiwa, bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni masu dorewa tare da bangaren Sin, bisa tushen mutunta juna, da amincewa juna, duba da yadda duniya ke fuskantar yanayi na tashe-tashen hankula da rashin tabbaci. Ya ce bangaren Birtaniya ba zai canza manufarsa kan batun Taiwan na kasar Sin ba. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *