Tsohon Sanatan Delta, Peter Nwaoboshi, ya rasu
[ad_1]
Tsohon Sanata Peter Nwaoboshi, wanda ya wakilci yankin Delta ta Arewa a Majalisar Tarayya, ya rasu.
Rahotanni sun ce ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Delta, Mista Festus Ahon ne, ya tabbatar da rasuwarsa a ranar Juma’a.
Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana baƙin cikinsa kan rasuwar Sanatan, inda bayyana cewa babban rashi ne ga Jihar, al’ummar Anioma da kuma Najeriya baki ɗaya.
Gwamnan, ya ce Nwaoboshi ya kasance jajirtacce kuma gwarzo mutum mai kare muradun al’ummar Anioma, tare da kasancewa shugaba mai daraja.
Gwamna Oborevwori ya ce, “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Delta, ina jimamin rasuwar abokina, Sanata Peter Onyelukachukwu Nwaoboshi.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalansa, al’ummar Anioma, jam’iyyar APC da duk waɗanda rasuwar ta shafa.”
Gwamnan ya bayyana irin rawar da Nwaoboshi ya taka a Majalisar Tarayya, musamman lokacin da ya kasance Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Neja Delta.
Ya ce marigayin ya yi ta fafutukar ganin an samu ci gaba da bunƙasa yankin Neja Delta da Jihar Delta.
Gwamna Oborevwori ya bayyana shi a matsayin shugaba na gari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa, jam’iyyarsa da ƙasarsa hidima.
Marigayin ya yi aiki a Majalisar Tarayya daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link