’Yan bindiga sun sace uwa da ‘ya’yanta 3 da wasu

[ad_1]



Rahotanni daga Jihar Kogi na bayyana cewa, wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane tara da suka haɗa da wata mata da ‘ya’yanta uku a ƙauyen Inele-Ugoh da ke unguwar Igah Ikeje a Ƙaramar hukumar Olamaboro ta jihar .

Lamarin dai ya afku ne da sanyin safiyar Juma’a inda wasu sama da ‘yan bindiga 40 ɗauke da makamai suka kutsa cikin unguwar.

Matar da ‘ya’yanta uku an ce suna kan hanyarsu ta zuwa wata unguwa domin yin jana’iza, sai ’yan bindigar suka tare su suka tafi da su cikin dajin.

Rahotannin sun kuma ce, an yi awon gaba da wasu mutane biyar daga gonakinsu a yayin harin.

Wani ganau ya ce adadin maharan da makaman da suke ɗauke da su sun tsorata ’yan banga na yankin daga tunkarar su.

Bayan kai harin, an ce al’ummar yankin sun aika da kiraye-kirayen gaggawa ga dakarun birgediya ta 12 na sojojin Najeriya da ke wani shingen bincike a yankin.

Sai dai sojojin sun isa ne bayan ’yan bindigar sun tsere zuwa cikin dajin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *