Ministan Wajen Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Iran Ta Wayar Tarho

[ad_1]

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya tattauna tare da takwaransa na kasar Iran, Seyed Abbas Araghchi a jiya Talata.

A yayin tattaunawar, Mr. Araghchi ya bayyana sabon yanayin da ake ciki a shiyyarsu, tare da nuna godiya ga kasar Sin bisa gudummawar jin kai da ta samar. A cewarsa, Iran na son ganin an dakatar da yaki daga dukkan fannoni a maimakon tsagaita bude wuta na wucin gadi. Ya kara da cewa, mashigin Hormuz ya kasance a bude ga kowa, inda jiragen ruwa ke iya wucewa cikin tsaro, amma ban da na kasashen da yakin ya shafa. Yana mai fatan ganin kasar Sin ta ci gaba da taka kyakkyawar rawa wajen wanzar da sulhu da kuma dakatar da yakin.

Mr. Wang Yi a nasa bangare ya nanata matsayin kasar Sin, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi a warware dukkanin matsaloli ta hanyar yin shawarwari a maimakon nuna karfin tuwo, wanda hakan ya dace da moriyar Iran da ma al’ummarta, tare da amsa kiran kasa da kasa. Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan matsayin adalci, tare da kin amincewa da keta ikon mulkin kai na kasashe, za ta kuma yi kokarin sulhuntawa a tsakanin sassan da abin ya shafa, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar. (Lubabatu Lei)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *