Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
[ad_1]
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe wasu mayaƙan ISWAP 11 a hare-haren da suka kai Jihohin Borno da Adamawa.
A wata sanarwa da rundunar haɗin gwiwa ta fitar a yau Talata, ta ce lamarin ya faru ne a jiya Litinin bayan da mayaƙan ISWAP suka kai wa sojojin harin kwanton ɓauna a kusa da Garin Giwa, ƙaramar hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Sanarwar ta ce sojojin sun daƙile harin, inda suka kashe mayaƙa takwas ciki har da kwamandojinsu biyu, tare da ƙwato makamai da babura.
Har ila yau, a Jihar Adamawa, dakarun sojin tare da taimakon mafarauta da ‘yan sa-kai sun kashe wasu mayaƙa uku sannan suka karɓe makamansu.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko akwai sojojin da suka rasa rayukansu a artabun ba.
Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link