Ƴansanda Sun Kama Mutane Uku Kan Siyan Motar Miliyan 75 Amma Suka Tura Kuɗin Bogi
[ad_1]
Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wasu mutane uku bisa zargin siyan wata motar alfarma ta amfani da tura kuɗi na bogi na naira miliyan 75 (₦75,000,000).
An bayyana sunayen waɗanda aka kama da Ibrahim Tijjani, Jamilu Auwal da Mohammed Nura Dauda. An kama su ne a ranar 28 ga Janairu, 2026, a unguwar Kabuga a Kano, bayan samun bayanan sirri daga jama’a, in ji rundunar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Layin Dogo A Babban Birnin Kano Na Naira tiriliyan 1
- CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika
A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce ana zargin mutanen sun sayi wata farar mota kirar Mercedes Benz GLE daga Gwarinpa, Abuja, ta hanyar amfani da hanyar saƙon tura kuɗi na ƙarya da wani Ibrahim Yahayawanda har yanzu ba a gano inda yake ba, ya aike da saƙon kuɗin.
‘Yansanda sun ce an kwato motar tare da miƙa ta ga Rundunar ‘Yansandan Babban Birnin Tarayya (FCT) domin ci gaba da bincike, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kamo wanda ake nema.
Kwamishinan ‘Yansandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai kira ga mazauna jihar da su kasance masu sa ido da kuma bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen hana aikata laifuka.
[ad_2]
Source link