Yadda Gwamnatin Tarayya Za Ta Habaka Fannin Aikin Noma A 2026 —Kwararru
[ad_1]
Yanayin noma a shekarar 2026, ya ta’allaka da irin mayar da hankalin da gwamnatin tarayya za ta yi, wajen kawo karshen manyan matsalolin da manoman kasar nan ke ci gaba da fuskanta, musamman duba da cewa; fannin na bayar da gagarumar gudunmawa, wajen samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin wannan kasa.
Hakan ne ya sanya, Jaridar BusinessDay, ta tattauna da wasu kwararru a fannin, inda suke yi karin haske a kan abubuwan da suka kamata gwamnatin ta mayar da hankali a kansu, domin habaka fannin na noma.
- Jakadan Sin: Cudanyar Al’adu Za Ta Taimaki Yunkurin Daidaita Hulda Tsakanin Sin Da Amurka
- Gobara Ta Hallaka Mutum 2, Ta Lalata Dukiya Ta Biliyan 1.59 A Bauchi
Masanan sun bayyana cewa, fannin na noman kasar, zai kara bunkasa ne kadai idan gwamnatin ta mayar da hankali wajen magance kalubalen rashin tsaro da samar wa da manoman tallafi da tabbatar da ganin ana yin noman har zuwa karshen shekara da kuma gayyato musu ruwa da tsaki a cikin fannin da samar masu da kayan aikin noma da sauransu.
Sama Musu Kayan Aiki A Farashi Mai Sauki:
Tsadar farashin kayan aikin noma, na daya daga cikin kalubalen da manoman kasar ke ci gaba da fuskanta, wanda kuma hakan ke ci gaba zama barazana ga sana’ar ta manoman da kuma shafar jarinsu..
Kazalika, wadannan matsaloli a shekarar 2025, sun haifar da karancin abinci a kasar tare da kuma haifar da hauhawar farashin kayan abinci da kuma dakile ribar da ya kamata manoman su samu.
Nijeriya dai, ta dogara ne a kan shigo da kayan abinci daga waje, musamman domin cike gibin da ake da shi na abinci a cikin kasar.
Bisa wasu alkaluma da cibiyar kididdiga ta kasa, wato NBS ta fitar, sun suna cewa; jimillar kayan abinci na naira tiriliyan 3.34, aka shigo da su cikin kasar nan daga watan Janairu zuwa na Satumbar 2025, wanda ya karu da kashi 23 cikin 100.
Manoman kasar, na ci gaba da kokawa kan yadda ake shigo da kayan abinci da rage samar da ayyukan yi ga fannin,” a cewarsa.
Magance Kalubalen Tabarbarewar Rashin Tsaro:
An shafe shekaru uku, fannin aikin noma na kasar nan na fuskantar matsalar sauyin yanayi.
Kazalika, akwai batun karancin ruwan sama da ambaliyar ruwan sama da ke shafar fannin, wanda hakan ke haifar da asarar biliyoyin nairori na jarin da manoman suka zuba a sana’ar tasu, musamman a Arewacin kasar nan.
Bugu da kari, wasu alkaluma da hukumar kasa da kasa da ke sanya ido kan afkuwar annoba, sun nuna cewa; a shekarar 2022 jimillar mutane miliyan 21.9 sauyin yanayi ya shafa a kasar, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutane 603 da kuma asarar da ta kai ta dala biliyan 4.2 daidai da naira biliyan 1.6.
Shi kuwa, shugaban kungiyar masu sarrafa takin zamani na gargajiya na kasa, Jude Obi ya sanar da cewa; tsananin zafin yanayi na shafar amfanin gona.
Karfafa Wa Manoma Gwiwa Don Yin Noma Har Zuwa Karshen Shekara:
Za a iya cimma hakan, idan har an samar wa da manoman kayan aikin noma na rani, musamman duba da yadda a duk shekara ake samun raguwar aikin noma a duk shekara, wanda hakan kuma ke shafar kudin shiga da manoman ke samu.
Hasashen da hukumar kula da ssmar da abinci ta duniya (FAO) a shekarar 2050 ta yi, ta ce yawan ruwan da duniya ke bukata, zai karu da kashi 50.
Bugu da kari, domin samun damar iya ciyar da yawan al’ummar kasar nan da abinci, akwai bukatar gwamnatin tarayya, ta samar da kyakkyawan yanayi ga manoman kasar, musamman ta hanyar samar musu da kayan aikin noma na rani, domin su kara habaka sana’ar tasu.
“Domin dawo da kima da kuma martabar aikin noma a kasar nan, ya zama wajibi gwamnatin tarayya, ta samar wa da manoman kayan aikin noma na zamani” in ji shugaban kungiyar manoma ta kasa, Ibrahim Kabir.
[ad_2]
Source link