Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Neja
Dakarun rundunar sojoji ta 22 Armored Brigade da ke aiki a ƙarƙashin Operation Park Strike V tare da haɗin gwiwar Jami’an tsaron gandun daji sun kashe wasu ’yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba a dajin Kainji da ke Ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja.
Hakazalika an samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3 da babura 4 daga hannun maharan.
Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 22 da ke Ilorin, Captain Stephen Nwankwo, a wata sanarwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce, ɗaya daga cikin jami’an da suke kula da gandun dajin yankin ya samu raunuka a harbin bindiga, amma ya fara samun sauƙi.
Wannan farmakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na samar da tsaro a dajin Kainji (KLNP) daga wuraren da ke da ’yan tada ƙayar baya.
Ya ƙara da cewa, an samu nasarar ne a safiyar ranar Alhamis 25 ga watan Satumba, 2025, lokacin da jami’an tsaro na haɗin gwiwa suka yi wa ’yan tada ƙayar bayan kwanton ɓauna a dajin Kainji.
Ya ce, “A ci gaba da ƙoƙarin da ake na samar da tsaro a dajin Kainji (KLNP) daga miyagu da ke haddasa rashin tsaro a yankin, sojojin na 22 Armored Brigade, da ke aiki a ƙarƙashin Operation Park Strike Ɓ, tare da jami’an gandun dajin Park Rangers, sun gudanar da wani samame na kwantan ɓauna a safiyar ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025.
“A bisa sahihan bayanan sirri, sojojin sun yi kwanton ɓauna a mashigar ’yan tada ƙayar bayan a Tungan Talle, Sashen Zugurma na wurin shaƙatawa da misalin ƙarfe 1:15 na safe.
“A yayin arangamar, sojojin sun yi artabu da ’yan ta’addan da musayar wuta, inda suka kashe wasu da ba a tabbatar da adadinsu ba, yayin da wasu suka samu raunuka, inda suka samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 3 da kuma babura 4.