Shekarar Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Afirka Ta 2026 Ta Bude Sabbin Hanyoyin Hadin Gwiwa
[ad_1]
A matsayin shekarar musayar al’adu da cudanyar jama’a tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afirka, shekarar bana ta bude sabbin hanyoyi na hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
Jaridar Le Soleil ta Senegal ce ta wallafa hakan a jiya Asabar, inda ta kara da cewa, sanya batutuwan da suka shafi bil’adama, da al’adu, da matasa a wani matsayi mafi muhimmanci, zai taimaka wajen inganta hadin gwiwa ga alkibla mai dorewa da karbuwar zamantakewa.
Bugu da kari, jaridar ta nuna cewa, dangantakar Afirka da Sin ta shaida kyawun tsare-tsare da aka aiwatar a shekarar 2025, kuma za ta shiga wani sabon mataki a shekarar nan ta 2026, wanda hakan zai daidaita ci gaban tattalin arziki da habaka karfin kwararru. Ta hanyar inganta fahimtar juna da zurfafa musayar al’adu, hadin gwiwar Afirka da Sin zai kara habaka, da kuma kaiwa ga magance kalubalen ci gaba mai dorewa da kuma yanayin duniya marar tabbas. (Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link