Farfadowar Halittun Ruwa A Kogin Yangtze Ta Nuna Kyakkyawan Yanayi
[ad_1]
Yau Talata, ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta Sin ta fitar da rahoto kan albarkatun halittun ruwa da yanayin rayuwarsu a kogin Yangtze na shekarar 2025. Rahoton ya nuna cewa farfadowar halittun ruwa gaba daya a kogin Yangtze ta yi matukar kyau, kuma aikin hana kamun kifi ya cimma sakamako mai kyau.
Tun daga ranar 1 ga Janairun shekarar 2021, an aiwatar da manufar hana kamun kifi na tsawon shekaru goma a cikin muhimman yankunan ruwan kogin Yangtze. A halin yanzu, nau’o’in halittun ruwa a kogin Yangtze suna ci gaba da karuwa. Daga 2021 zuwa 2025, an sa ido kan jimillar nau’ikan kifaye 351 a kogin Yangtze, inda aka samu karin nau’ikan kifaye 43 idan aka kwatanta da lokacin da ba a hana kamun kifi ba, wato daga 2017 zuwa 2020.(Safiyah Ma)
[ad_2]
Source link