’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja

[ad_1]



’Yan bindiga sun kai wa wata mota hari a kan hanyar Tegina zuwa Kontagora a Jihar Neja, inda suka jikkata mutum biyu.

Harin ya faru ne a Tudun-Fulani bayan direban motar ya ƙi tsayawa lokacin da ’yan bindigar suka buƙaci ya tsaya.

Rashin tsayawarsa ya sa maharan suka buɗe wa motar wuta, inda suka jikkata fasinjoji biyu da ke zaune a kujerar gaba.

Wannan lamarin ya faru ne bayan sa’o’i da ’yan bindigar suka sace wasu makiyaya a garin Usalle da daren ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewar ’yan bindigar sun tura makiyayan bakin hanya sannan suka yi yunƙurin amfani da su wajen tare motocin da ke wucewa a kusa da ƙauyen Samaza Sauri da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora.

Wani mutum ya ce: “Da misalin ƙarfe 10:30 na dare, sun sace wasu makiyaya a Usalle.

“Bayan nan suka tare hanya a Samaza Sauri, sun buɗe wa motoci da ke zuwa Kontagora wuta, inda suka jikkata mutum biyu a ƙafafunsu.”

Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, ta tabbatar da aukuwar harin.

Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya ce: “A ranar 11/09/2025 da misalin ƙarfe 12:15 na dare, wasu ’yan bindiga sun yi ƙoƙarin tare wata mota a Tudun-Fulani.

“Direban ya tsere, amma sun buɗe musu wuta tare da jikkata fasinjoji biyu. An kai su asibiti, amma ba a sace kowa ba.”

’Yan sanda da jami’an tsaro sun isa wajen da harin ya auku, amma ’yan bindigar sun tsere cikin daji.

A wani harin kuma, ’yan bindiga sun shiga ƙauyukan Uzange da Matachibu a gundumar Masuga da ke Ƙaramar Hukumar Kontagora, inda suka sace mutum uku cikin daren ranar Alhamis.

Mazauna Ƙananan Hukumomin Kontagora, Mariga, da Magama, sun bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga sun ƙaru a baya-bayan nan, inda suka ce an sace mutane da dama tare da yin awon gaba da ɗaruruwan shanu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *