An sace tumaki 1,400 da kashe makiyayi a Borno

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa wasu da ake zargin ’yan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai hari wani matsugunin makiyaya a ƙaramar hukumar Konduga, inda suka kashe makiyayi guda tare da sace tumaki kusan 1,400.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Wuturo, wani matsugunin makiyaya kusa da garin Konduga. Daso ya ce mambobin ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ne suka kai rahoton harin zuwa ofishin ’yan sanda na Konduga.

A cewar sanarwar, maharan sun isa matsugunin ne da daddare a kan babura.

“Bayan samun rahoto daga ƙungiyar Miyetti Allah ta Konduga a ofishin ’yan sanda na Konduga cewa a ranar 10 ga Maris, 2026, da misalin ƙarfe 22:30 na dare, wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a kan babura biyar sun kutsa kai cikin matsugunin,” in ji sanarwar.

Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa, an kashe mutum guda yayin harin, yayin da wani kuma ya samu raunuka.

“Binciken farko ya nuna cewa yayin harin, Ahmadu Baida, mai shekaru 40, ya samu raunukan harbin bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwarsa, yayin da Mohammadu Baida, mai shekara 30, ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu. Maharan sun kuma yi awon gaba da tumaki kusan dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400) na makiyayan,” in ji sanarwar.

An tura jami’an tsaro zuwa yankin jim kaɗan bayan samun rahoton.

“Bayan samun rahoton, wata haɗin guiwar tawagar ’yan sanda, sojoji da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, ciki har da jami’an sa-kai (Civilian JTF) da mafarauta, ƙarƙashin jagorancin baturen ’yan sanda na Konduga, sun gaggauta isa wurin,” in ji Daso.

Ya kara da cewa an kai wadanda abin ya shafa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikinsu.

“An ɗauke waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti inda likita ya tabbatar da mutuwar Ahmadu Baida lokacin da aka isa, yayin da shi kuma wanda ya ji rauni yake karbar magani kuma yana samun sauki,” in ji shi.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Naziru Abdulmajid, ya yi Allah-wadai da harin, sannan ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamacin. Kakakin rundunar ya ce tuni hukumomin tsaro suka fara gudanar da bincike da nufin kamo waɗanda suka aikata laifin tare da dawo da dabbobin da aka sace.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *