Raheem Sterling Ya Bar Chelsea Bayan Shafe Shekaru 3

[ad_1]

Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea, Raheem Sterling ya yanke shawarar barin ƙungiyar a wani hukuncin ƙashin kai da ya yanke, duk da cewar akwai sauran watanni 18 a kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 31, inda yake karɓar Yuro dubu 325 a mako a matsayin albashi

Sterling ya bar ƙungiyar ta Stamford Bridge bayan shafe shekaru uku da rabi.

  • Gwarzon 2025: Malamin Firamare Ya Samu Kyautar N50m Da Sabon Gida
  • Firaministan Kasar Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin

A shekarar 2022 Sterling ya je Chelsea daga Manchester City a kan kuɗi Yuro miliyan 47.

Chelsea ta sanar da tashin Sterling a wani rubutu da ta yi a shafinta na sada zumunta.

“Muna godiya ga Raheem a kan gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake ɗan wasan Chelsea kuma muna yi masa fatan alheri a mataki na gaba a rayuwarsa,”.

Ɗan wasan na Ingila ya buga wa Chelsea wasanni 81, Raheem ya koma ɗaukar horo tare da matasan ‘yan wasan ƙungiyar yayin da yake neman dawowa da kuzarinsa, ƙungiyoyi da dama, ciki har da Juventus da Bayer Leverkusen, sun yi ƙoƙarin cimma yarjejeniyar sayen ɗan wasan a lokacin da yiwuwar sauya sheƙarsa zuwa Fulham bai yiwu ba.

Rahotanni sun nuna cewar Sterling, wanda ya fara buga wasa a Liverpool kuma ya lashe kofuna 13 jimilla, yana sha’awar ci gaba da zama a Landan amma kuma a shirye yake ya buga wasa a ko ina idan ya samu ƙungiyar da za ta ɗauke shi yayinbda kasuwar musayar ‘yan kwallo take buɗe a halin yanzu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *