Yunƙurin Juyin Mulki: Hafsoshin Soji 16 Za Su Fuskanci Hukunci
[ad_1]
Hafsoshin Sojin Nijeriya aƙalla 16 ne za su fuskanci hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai bisa laifin yunƙurin hamɓarar da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa binciken da ta kammala bayan tsare waɗanda ake zargin ya same su da laifin yunƙurin kifar da gwamnati.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 11 Yayin Da Ake Kallon Ƙwallo A Mexico
- Da Gaske Ne Babu Tashar Samar Da Lantarki Ta Karfin Iska A Kasar Sin?
Wasu tsofaffin Hafsoshin sojin Nijeriya sun bayyana cewa hukuncin kisa shi ne abin da dokar aikin sojin ƙasar ta tanada kan duk wanda aka samu da hannu a yunƙurin juyin mulki.
A watan Oktoban bara ne rahoto ya ɓulla cewa, Rundunar Sojin Nijeriya, ta hannun Hukumar Binciken Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta tsare wasu hafsoshinta 16 masu muƙamin Kyaftin zuwa Birgediya-Janar kan zargin yunƙurin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.
An ruwaito a ranar Litinin cewa kwamitin da rundunar ta kafa ya kammala bincikensa tare da miƙa rahotonsa ga Shugaba Tinubu domin ɗaukar mataki na gaba.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya, Manjo-Janar Samaila Uba, ya tabbatar cewa kwamitin ya miƙa rahotonsa ga “mahukuntan da suka dace.”
Sanarwar da Manjo-Janar Samaila Uba ya fitar a ranar Litinin ta ce za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotun soji domin yanke musu hukuncin da dokokin aikin soji suka tanadar.
Ya bayyana cewa an sanar da jama’a halin da ake ciki ne domin komai ya kasance a fili da kuma tabbatar da adalci, a yayin da rundunar za ta kiyaye ƙa’idojin aikinta cikin ƙwarewa, da kuma biyayya da kare dokar ƙasa.
Ya ce doka ce ta tanadar da matakan ladabtarwa da aka ɗauka domin tabbatar da ɗa’a da kuma ƙwarewa a tsakanin jami’an rundunar.
[ad_2]
Source link