Ana Maraba Da ‘Yan Jarida Na Cikin Gida Da Na Ketare Ga Taron NPC da CPPCC Da Sin Za Ta Gudanar

[ad_1]

Za a bude zaure na 4 na majalisar wakilan jama’ar Sin karo na 14 wato NPC a ranar 5 ga watan Maris na shekarar nan ta 2026. Sannan za a kaddamar da taro karo na 4 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin na 14 wato CPPCC a ranar 4 ga watan Maris na shekarar a birnin Beijing. A yau Talata ne ofisoshin kwamitin zartarwa na NPC da CPPCC suka bayyana cewa, ana maraba da ‘yan jarida na cikin gida da na ketare da su labarta wadannan taruka biyu.

’Yan jarida za su iya neman labarai na fuska da fuska a yayin tarukan, tare da hada hanyoyi daban-daban. Taron zai ci gaba da rike ruhin bude kofa da bayyana gaskiya, don baiwa ‘yan jarida na cikin gida da na ketare hidimar yin hira da bayar da rahoto. ‘Yan jarida na ketare masu ziyarar wucin gadi zuwa Sin, ya kamata su gabatar da aniyar hakan ga ofishin jakadancin Sin dake kasashensu, ko hukumomin samar da biza wadanda suka samu izini daga wajen ma’aikatar harkokin waje ta Sin. Ranar karshe ta yin rajistar ‘yan jaridar ita ce ran uku ga watan Fabrairu mai zuwa. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *