‘Yan Nijeriya Miliyan 140 Za Su Faɗa Ƙagin Talauci A 2026 – Masani

[ad_1]

Masanin tattalin arziƙi, Franklin Ngwu, ya yi gargaɗin cewa aƙalla mutane miliyan 140 a Nijeriya na iya faɗawa cikin ƙangin talauci a shekarar 2026 duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar.

Ngwu, wanda shi ne Daraktan Public Sector Initiative a Legas Business School, ya bayyana haka a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise a ranar Litinin.

  • An Fara Tafiye-Tafiye Na Bikin Bazara Na Sin A Yau
  • An Fitar Da Sakon Bidiyo Na Yayata Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Afirka Ta Kudu

Ya ce Nijeriya ta buƙaci gyare-gyare, amma yadda aka aiwatar da su musamman cire tallafin man fetur da kuma rage dajarar naira, ya ƙara jefa mutane da hawa cikin ƙangin wahala.

A cewarsa, rashin aikin yi, talauci, da bashin gwamnati na ƙaruwa, duk da cewa kuɗaɗen shiga na gwamnati suna ƙaruwa kuma ana cewa hauhawar farashi na raguwa.

Ngwu ya ƙara da cewa ainihin tabbatar da sauye-sauyen shi ne yadda talakawa suke ji, kuma da yawa suna cikin wahala.

Ya kawo rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya nuna cewa mutane miliyan 30 na iya faɗawa cikin talauci a wannan shekarar, wanda zai kawo adadin talakawa zuwa kusan miliyan 140 a shekarar 2026.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *