Har Yanzu Ba Mu Fitar da Rai Kan Samun Tikitin Kofin Duniya Ba — NFF
[ad_1]
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayyana cewa har yanzu ba ta fitar da rai kan batun samun tikitin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 ba, yayin da take jiran hukuncin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) za ta yanke kan ƙorafin da ta shigar kan Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo).
NFF ta zargi tawagar Kongo da amfani da ’yan wasan da ba su cancanta ba a wasan karshe na neman tikitin gasar da aka buga a watan Nuwamba. A wancan karawar, tawagar Leopards ta Kongo ta doke Super Eagles ta Nijeriya a bugun fanareti, lamarin da ya sa NFF ta garzaya FIFA da takardar ƙorafi makonni bayan wasan.
- AFCON 2025: Dalilin Da Ya Sa Super Eagles Ba Ta Jira Bikin Karɓar Kyautar Tagulla Ba – NFF
- Ana Maraba Da ‘Yan Jarida Na Cikin Gida Da Na Ketare Ga Taron NPC da CPPCC Da Sin Za Ta Gudanar
Sakataren Janar na NFF, Dakta Sanusi Mohammed, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Brila FM, inda ya ce hukumar ba ta ɗauki mataki a banza ba, sai dai tana bin ƙa’ida domin a binciki zargin da ta gabatar.
“Ba ma shiga abin da muka san aikin banza ne. Yanzu haka muna da ƙara a gaban FIFA, muna jiran hukuncin da za a yanke kan waɗanda muka zarga da aikata ba daidai ba,” in ji Sanusi, yana mai jaddada cewa NFF na fatan adalci zai bayyana a ƙarshe.
[ad_2]
Source link