‘Yan Bindiga: ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Uku Gami Da Kwato Bindigar AK-47 A Gombe

[ad_1]

Rundunar ‘Yansandan Jihar Gombe ta ceto mutum uku da aka sace tare da kwato bindigogi AK-47 guda biyu, bayan wani hari da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a Gundumar Pindiga da ke Karamar Hukumar Akko a jihar.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce harin ya faru ne a kauyukan Rahama, Lambo da Garin Galadima.

  • An Nada Liu Xianfa Wakilin Musamman Na Gwamnatin Sin Kan Harkokin Afirka
  • Yadda Buƙatun Kwankwaso Suka Tarwatsa Yiwuwar Haɗin Gwuiwa Da APC

Sanarwar ta bayyana cewa harin ya fara ne da safiyar ranar 24 ga Janairu, 2026.

“Ranar 24/01/2026 da misalin karfe 02:00 na dare, bayanan da aka samu sun nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Rahama ta hanyar Gagarabami, inda suka harbe tare da kashe Tela Bello Ahmadu, mai shekaru 70,” in ji ‘yansanda.

Sanarwar ta kara da cewa maharan daga bisani sun sace ‘ya’yansa biyu, Saleh Tela (mai shekaru 25) da Abdullahi Tela (mai shekaru 35).

Abdullahi ya ce wannan kungiya ta tafi kauyen Lambo da misalin karfe 3:40 na dare, inda suka sace wasu mazauna uku.

“Sun sace Babayo Garba, mai shekaru 30, Malam Abba Musa, mai shekaru 45, da Baayo Bayi, mai shekaru 20,” in ji shi.

Bayan karbar kiran agaji, kungiyoyin sintirin ‘yansanda karkashin Operation Hattara, tare da hadin gwiwar mafarauta da ‘yan sa-kai, sun tafi wurin suka yi arangama da maharan.

“Yayin aikin, Baayo Bayi, abin takaici, ya fada cikin musayar wuta kuma daga baya aka tabbatar da rasuwarsa, yayin da Babayo Garba da Malam Abba Musaaka ceto su lafiya,” in ji sanarwar.

‘Yansanda sun ce an kashe wasu daga cikin maharan uku yayin musayar wuta, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji, inda ake zargin sun samu raunuka daga harbin bindiga.

Abubuwan da aka kwato daga aikin sun hada da: bindigogi AK-47 guda biyu, jigida guda hudu, harsasai 68 na 7.62mm, harsasai 120 da aka harba, babura guda hudu da kuma kudi Naira 2,300.

An kai wadanda aka ceto asibiti domin gwajin lafiya.

Rundunar ta ce an kara kokari wajen kama maharan da suka tsere, sannan za a sanar da al’umma da zarar an samu ci gaba.

Kwamishinan ‘Yansanda, CP Umar Ahmed Chuso, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar na nan daram wajen tabbatar da tsaro.

“Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar ba, sannan ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci ga ‘yansanda,” in ji sanarwar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *