’Yansanda Sun Ƙwato Motocin Sata 3 Tare Da Kama Mutane 5 A Kano

[ad_1]

Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta ƙwato motocin sata uku tare da kama mutane biyar da ake zargi da aikata fashi da kuma satar motoci.

’Yansanda sun ce jami’ansu sun tare wata mota ƙirar Toyota Corolla da aka sace a yankin Hotoro NNPC a ranar 3 ga watan Janairu, 2026, inda suka kama mutum guda ɗaya.

  • Shirin Ceto Zamfara Na Samun Nasara, Yayin Da Gwamna Lawal Ke Duba Ayyuka A Shinkafi
  • Za Mu Baza Ƙarin Jami’anmu A Faɗin Nijeriya Don Samar Da Tsaro – Sojoji

Bincike ya kai ga kama wasu mutane huɗu, waɗanda suka amsa cewa su ne suka sace motar daga Bauchi tare da wata mota, Honda Pilot mallakin Gwamnatin Jihar Bauchi.

An samu nasarar ƙwato dukkanin motocin.

A wani lamari daban, ’yansanda sun kuma ƙwato wata mota ƙirar Toyota Sienna da ake zargin ta sata ce, wadda aka tsinta a yankin Hotoro ta Arewa a ranar 6 ga watan Janairu, 2026.

Rundunar ta buƙaci masu motocin da aka ƙwato su je hedikwatar ’yansandan Jihar Kano da hujja domin karɓar motocinsu.

Kwamishinan ’yansandan jihar ya yaba wa jami’an rundunar bisa ƙwazonsu, tare da gode wa al’ummar jihar kan haɗin kai da suke bai wa hukumomin tsaro.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *