Dangote ya Janye ƙorafin da ya shigar kan tsohon Shugaban NMMPRA
[ad_1]
Hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, ya janye ƙorafin da ya shigar a Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) kan tsoho Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai Fetur ta Kasa (NMMPRA), Farouk Ahmed.
Lauyan Dangote, Ogwu Onoja ne, ya aike takardar janye ƙorafin.
Ya janye ƙorafin ne bayan wata hukumar gwamnati ta ɗauki alhakin ci gaba da bincike game da zargin.
A watan Disamban 2025 ne, Dangote ya buƙaci ICPC ta binciki Ahmed kan zargin amfani da muƙaminsa wajen satar kuɗaɗen gwamnati.
Dangote ya ce yana da hujjoji da suka tabbatar da zarginsa.
Mai magana da yawun ICPC, John Odey, ya tabbatar da janye ƙorafin. amma ya ce hukumar za ta ci gaba da bincike a kan lamarin.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da bincike domin yin gaskiya, adalci, da yaƙi da cin hanci a Najeriya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link