ADC Ta Gargadi Magoya Bayan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Gabanin Zaben Fitar Da Gwani
[ad_1]
An yi kiran ga goyon bayan duk ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar hadaka ta ADC da su daina yawan furta maganan da za su iya jawo rarrauwar kai, musamman ma magoya bayan Mista Peter Obi a gaban zabukan fad da gwai da za a yi a watan Yuni, 2026.
Jam’iyyar adawa ta yi wannan gargadin ne ta hanyar wani shirin tattaunawa na sauti kai tsaye da ya shafi halin da kasar ke ciki.
- An Nada Liu Xianfa Wakilin Musamman Na Gwamnatin Sin Kan Harkokin Afirka
- CGI Babandede Mai Ritaya A Mizanin Kyawawan Halaye Da Kwazon Aiki
Jam’iyyar ta kuma lura cewa gudanar da zaben 2027 a shekarar 2026 kamar yadda ake shawar yi zai zama tamkar takobi mai kaifi biyu gare ta, inda ta jaddada cewa jam’iyyar za ta sha wahala wajen yin shirin zaben.
Duk da haka, ta nuna cewa gudanar da zaben kafin lokaci zai yi aiki ne ga jam’iyya a daya bangaren.
Sakataren yada labarai na kasa na ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ya yi wasu tattaunawa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar jam’iyyar LP a zaben 2023, Mista Peter Obi da tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da kuma wasu kamar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai kan bukatar karfafa hadin kai da mayar da hankali da kuma jajircewar da za ta tabbatar da nasara a zaben da ke tafe.
Abdulllahi ya ce, “Na dauki tsawon lokaci ina magana da Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi wadanda suka nuna sha’awar yin takarar shugaban kasa a jam’iyyarmu, haka kuma na tattauna da irin su Malam Nasir El-Rufai don karfafa jam’iyyarmu da hadin kai don seta alkiblar wannan kasa ta zama wuri mafi kyau.
“Dukkan shugabanninmu sun sani game da aikin da ke gabanmu, kuma kowannensu ya himmatu wajen tabbatar da cewa mun ci wannan zaben.”
Bugu da kari a kan haka, ya ce ko za a gudanar da zabe a wannan shekara ko shekara mai zuwa zai kasance aiki biyu ga jam’iyyar.
Sakataren jam’iyyar ya kuma ce suna daukar zaben kananan hukumomin Abuja da matukar muhimmanci, yana nuna cewa sun kasa samun nasara a zaben cike guri a Jihar Anambra, don haka, suke wannan bayanin.
Haka kuma ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin Jihar Legas ke kwatanta ma’aikatan gwamnati da lambar shaida ta kasa don yin rajista a matsayin mambobin APC.
A wani labarin mai kama da wannan, ADC ta rubuta wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wasikar na neman daga zaben kanana hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja da aka shirya a ranar Asabar, 21 ga Fabrairu, 2026, saboda azumin watab Ramadan.
A cikin wasikar da aka rubuta a ranar 22 ga Janairu, 2026, wacce ta samu sa hannun shugaban jam’iyyar, Sanata Dabid A. B. Mark, da sakataren jam’iyyar, Ogbeni Rauf Aregbesola, jam’iyyar ta jawo hankalin hukumar zabe kan cewa, ranar zaben da aka tsara ana cikin lokacin azumin Ramadan, wanda mafi yawan masu zabe na iya kaurace masa.
ADC ta rabuta a cikin wasikar cewa, dangane daukar muhimmancin al’adu da addini a wannan lokaci ya zama dole a sake duba ranar zabe. Don haka, jam’iyyar ta roki INEC cikin girmamawa ta jinkirta zaben zuwa bayan watan Ramadan.
Wasikar ta kara jaddada cewa bukatar ta samo asali ne daga bukatar kare hadin kai a tsarin zabe, inda ta bayyana cewa an yi ta ne domin cimma tsarin zabe mai tsari wanda ke ba dukkan ‘yan kasa ‘yancisu ba tare da la’akari da addini ba da damar amfani da cikakkiyar hakkokinsu na ‘yan ba tare da wani kuntatawa ko rashin fa’ida ba.
[ad_2]
Source link