Gobara ta ƙone shaguna a Kasuwar Sabuwar Mil 3

[ad_1]



Wata mummunar gobara a kasuwar Sabuwar Mil 3 da ke kan hanyar Gombe–Yola, ta cinye shaguna, kwantainoni da wuraren kasuwanci da dama, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa cikin asara mai yawa.

Gobarar ta faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na asubahin daren Juma’a, inda wutar ta bazu cikin sauri ta kama jerin shaguna, gidajen cin abinci da ƙananan kwantaina kafin jami’an kashe gobara su samu nasarar shawo kanta.

Zuwa safiyar Asabar, yawancin yankin kasuwancin ya koma toka.

Binciken farko ya nuna cewa sama da kashi 80 cikin 100 na yankin kasuwancin ya lalace, lamarin da ya haddasa asarar kaya da dukiya ga ’yan kasuwa da dama.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa gobarar ta tashi ba zato ba tsammani, kuma cikin ’yan mintuna kaɗan ta ƙara ƙarfi.

Mai taimaka wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na musamman kan harkokin tsaro da hulɗar gwamnatoci, Yusuf Musa Danbayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce babu wanda ya rasa ransa.

A cewarsa, “Duk da girman asarar da aka yi, muna godiya ga Allah domin babu rai da ya salwanta ko wanda ya ji rauni.”

Ya yaba wa hukumomin tsaro bisa gaggawar ɗaukar mataki, inda ya ce jami’an ’yan sanda daga sashen Tumfure da Pantami tare da Operation Hattara sun iso da wuri domin tsare yankin da kuma kare aukuwar wata matsala.

Haka kuma ya jinjinawa jami’an kashe gobara bisa ƙoƙarin da suka yi ba tare da gajiyawa ba.

Danbayo ya bayyana cewa Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, ta Jami’ar Jihar Gombe da ƙungiyar masu safarar ruwa sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da motocin kashe gobara da ruwa akai-akai har aka shawo kan wutar.

Ya ƙara da cewa ’yan kasuwa da masu taimakon jama’a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Auwal Abdulkadir, Shugaban Mile 3, sun bayar da gudunmawa wajen kare dukiyoyi da kuma hana wutar bazuwa zuwa wuraren da ke kusa.

Wasu daga cikin ’yan kasuwar da abin ya shafa sun bayyana alhini bisa asarar da suka yi, amma suka gode wa Allah da babu wanda ya mutu. Sun kuma yaba da gaggawar jami’an kashe gobara wajen shawo kan lamarin.

Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta bakin kakakinta, DSP Buhari Abdullahi, bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *