2027: Watsi Da Muslim-muslim Tiket Zai Iya Raunata APC — Ministar Al’adu
[ad_1]
Ministar raya al’adu da yawon bude ido da tattalin arzikin kirkire-kirkire, Hannatu Musawa, ta yi gargadin cewa jam’iyyar APC za ta fuskanci barazanar a zaben 2027 idan ta yi watsi da Musulmin-muslim tiket a sake takarar Shugaban kasa Bola Tinubu.
Hannatu ta yi wannan gargadin ne a cikin wani tattauawa ta musamman da dan jarida Seun Okinbaloye, yayin da ake kara yawan jita-jitar cewa jam’iyyar mai mulki na iya la’akari da sauya tikitin Musulmi-Musulmi da aka yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a 2023.
- An Nada Liu Xianfa Wakilin Musamman Na Gwamnatin Sin Kan Harkokin Afirka
- Fasahar Electronic Call-up Da NPA Ta Wanzar Ta Samar Da Sauki —Tsohon Kwaminsihan Sufuri
A cewar ministar, cire Kashim Shettima ko maye gurbinsa da abokin takara Musulmi wanda ba na Arewacin Nijeriya ba zai zama babban kalubale na siyasa ga APC, musamman a jihohin arewacin kasar.
“Idan babu Musulmi Bahause ko Fulani ko Kanuri a wannan tikitin, hakan zai haifar da cikas. Wannan shi ne gaskiyar yadda mutane ke tunani,” in ji Hannatu.
Ta jaddada cewa siyasa a Arewacin Nijeriya ta tsayu sosai, tana gargadin cewa yanke shawara ba tare da cikakken fahimtar yankin ba na iya jefa kasa ciki matsala.
“Asalin jihohin arewa kamar Katsina, Kano, Kaduna, Kebbi, Jigawa, Zamfara da Sakkwato, suna fahimtar siyasa a mataki mai zurfi sosai. A wannan yanki, siyasa hanya ce ta rayuwa. Mutane na jira duk bayan shekaru hudu don su tsaya a layi su kada kuri’a saboda a can suke jin suna da tasiri,” in ji ta.
Hannatu ta yi watsi da ikirarin cewa APC za ta iya samun narasa a zabe n shugabancin kasa cikin sauki ba tare da wani kalubale ba, tana bayyana irin wannan zato a matsayin rashin sanin siyasa.
“Ina tunani cewa idan muka yi wasa da sauya tsarin abin da muke da shi yanzu, hakan zai zama matsala. Mutanen da ke ba da shawara akasin haka watakila ba su fahimci yadda siyasa ke aiki a Arewa ba,” in ji ta.
Game da maganganu kan karuwar hadin gwiwar ‘yan adawa kafin 2027, Hannatu ta ce ba ta ganin tsarin jam’iyyun ‘yan adawa na yanzu zai iya kifar da Shugaba Tinubu da mataimakinsa Shettima ba.
Ta bayyana ‘yan adawar a matsayin wadanda suka samu rarrabun kawuna sakamakon rikicin shugabanci mai zafi a tsakaisu.
Yayin da ta amince cewa ‘yan adawa suna ci gaba da tafiya babu tasiri, ta tabbatar da cewa APC na da kwarin gwiwa na ci gaba da rike iko a kasar nan.
Hannatu ta kara da cewa ko da yake APC na maraba da jam’iyyun adawa don ci gaban dimokiradiyya, jam’iyyar mai mulki tana mai da hankali kan karfafa tushen siyasarta kafin zaben 2027.
[ad_2]
Source link