China ta musanta bai wa Iran tallafin soji




Gwamnatin China ta musanta rahotannin da ke cewa tana bai wa Iran tallafin soja, tana mai jaddada cewa goyon bayanta ya taƙaita ne ga matakin siyasa da diflomasiyya kaɗai.

China na shigo da kusan kashi 70 cikin 100 na man fetur da take amfani da shi, inda kusan rabin hakan ke biyowa ta Mashigar Hormuz.

Wani ɓangare mai yawa na man na fitowa ne daga Iran, sai kuma wasu ƙasashen yankin da suka haɗa da Iraƙi, Saudiyya da Kuwait.

Sai dai Beijing ta ce ko tantama babu tana sa ido kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara cike da damuwa matuƙa.

Ta kuma yi kakkausar suka ga matakan da Amurka da Isra’ila suka ɗauka, tana mai cewa tattaunawar nukiliya da ake yi da Iran tana tafiya yadda ya kamata kafin rikicin ya ɓarke.

Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi, ya tattauna ta waya a ranar Litinin da ministocin harkokin wajen Oman, Iran da Faransa.

A cewarsa, matakan Amurka da Isra’ila ne suka kawo tsaiko a yarjejeniyar diflomasiyyar da ake yi, lamarin da ya jefa yankin cikin wani yanayi da ya kira mai wuyar gyarawa.

China na ci gaba da kira da a tsagaita wuta tare da komawa teburin sulhu.

Duk da cewa China na daga cikin manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arzikin da ke da alaƙa mai ƙarfi da Iran, musamman ta fuskar kasuwanci, Beijing ta bayyana Iran a matsayin abokiyar hulɗa, tare da goyon bayan haƙƙinta na kare ƙasarta da muradunta.

Sai dai Wang Yi bai nuna goyon baya ga duk wani matakin ramuwar gayya daga Iran ba.

Yayin da aka tambaye shi game da yiwuwar taimakon soja, ma’aikatar harkokin wajen China ta musanta zargin cewa tana bai wa Iran makamai ko wani tallafin soja, tana mai cewa goyon bayanta ya tsaya ne kan siyasa da ƙarfafa gwiwa kawai.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *