JIBWIS ta dakatar da tafsirin Sheikh Alƙali Zariya saboda sukar gwamnati

[ad_1]



Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Iqamatissunnah (JIBWIS) ta sanar da dakatar da tafsirin Ramadan da Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zaria ke gabatarwa a Masallacin Mokas da ke Damaturu, Jihar Yobe.

JIBWIS ta ce an dakatar da Sheikh Alƙali ne bisa umarnin Shugaban Majalisar Malamai na ƙasa, Muhammad Sani Yahya Jingir.

A sanarwar da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa an turo malamin ne daga hedikwatar ƙasa da ke Jos, kamar yadda aka saba yi tsawon shekaru 35 da suka gabata.

Sheikh Alƙali ya fara tafsirin ne tun daga farkon watan Ramadan, inda ya gabatar da shi na tsawon kwanaki 11 kafin a dakatar da shi a ranar 12 ga Ramadan 1447 Hijiriyya.

Ƙungiyar ta ce matakin ya biyo bayan wasu huɗubobi da nasihohi da malamin ya gabatar a wurare daban-daban, ciki har da hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Yobe, da Masallacin Alimarami, da kuma tafsirin da ya yi a Masallacin Mokas sanye da kayan agaji.

A cewar sanarwar, salon da malamin ya yi amfani da shi na kiran sunayen mutane da yin tsinuwa ya saɓa wa tsarin karantawar JIBWIS.

Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar 14 ga Ramadan, Sheikh Jingir ya kira malamin tare da mataimakin shugaban majalisar malamai na Jihar Yobe da wakilan Ƙaramar Hukumar Damaturu, inda aka tattauna lamarin.

Daga bisani aka yanke shawarar cewa ci gaba da tafsirin ba alkhairi ba, lamarin da ya sanya aka dakatar da malamin daga karatuttuka a Damaturu.

Ƙungiyar ta kuma sanar da cewa Sheikh Alƙali ya amince cewa ya yi kuskure, tare da ba da bai wa shugabannin ƙungiyar haƙuri da al’umma baki ɗaya kan abin da ya faru.

Aminiya ta ruwaito cewa, a wasu karatuttuka da Sheikh Alƙali ya gabatar a bayan nan, ya soki gwamnatin Najeriya ciki har da shugaban ƙasa, gwamnoni, jami’an tsaro da sauransu kan matsalar tsaron da ake fuskanta a ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *