DSS Ta Kama Wasu Jami’an Tsaro Kan Zargin Taimaka Wa El-Rufai

[ad_1]

Hukumar tsaron farin kaya (DSS), ta sanar da kama wasu jami’an tsaro da ake zargi da karɓar cin hanci domin bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, damar guje wa kama.

DSS ta ce bayan bincike, ta gano jami’ai biyar da suka haɗa da ɗansanda, jami’in DSS, jami’in shige da fice da kuma wasu jami’an tsaron filin jirgin sama da laifin karɓar cin hanci.

  • Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Bukatar Tsoffin Kwamishinonin Kano Na Riƙe Motocin Gwamnati
  • Gwamna Dauda Ya Yaba Da Yadda Aiki Ke Tafiya A Babban Filin Wasa Na Gusau

An miƙa su ga hukumar ICPC domin ci gaba da bincike.

Hukumar ta kuma ce akwai wasu jami’an da aka kama, amma ba a same su da laifin karɓar kuɗi ba.

Sai dai an zarge su da bari El-Rufai ya fice daga filin jirgin ba tare da bin ƙa’ida ba.

A baya, jami’an DSS sun yi ƙoƙarin kama El-Rufai a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe bayan dawowarsa daga Masar, amma hakan bai yi nasara ba.

DSS ta ce ta shigar da ƙara a kansa kan wasu zarge-zarge.

Sai dai ba a gabatar da shi a kotu ba a ranar da aka tsara, domin yana hannun ICPC inda ta me bincike a kansa.

El-Rufai ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *