Wane ne Ali Larijani, babban jami’in tsaron Iran da Isra’ila ta kashe?

[ad_1]



A ranar Talata, 17 ga watan Maris, Ministan Tsaron Isra’ila Israel Katz, ya iƙirarin cewa an kashe Ali Larijani, daya daga cikin manyan shugabannin Iran, tare da Janar Gholamréza Soleimani, kwamandan rundunar Bassidj, bayan hare-haren da sojojin ƙasarsa suka kai a cikin daren jiya a Iran.

A cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa Katz ya bayyana cewa shugaban rundunar sojin Isra’ila ya tabbatar masa da mutuwar Larijani, wanda shi ne sakataren Majalisar Tsaron Iran, da kuma Soleimani, shugaban rundunar Bassidj, wadda ake kallon ta a matsayin hukumar da ake amfani da ita don murƙushe.

Tun bayan mutuwar Khamenei, Larijani ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƙusoshi a gwamnatin Iran, kuma ana ɗaukar sa a matsayin wanda ke yanke manyan shawarwari tare da jagorantar hare-hare da ake kai wa Isra’ila da ƙasashen yankin Gulf.

Sai dai hukumomin Iran ba su gaskata ko kuma musanta wannan labari ba, hasali ma an wallafa wata wasiƙa daga shufukan Ali Larijani na X da kuma Instagram domin girmama sojojin Iran da suka mutu a wannan yaƙi.

Amma da yammacin nan, mahukuntan ƙasar Iran sun tabbatar da mutuwar Larijani.

Wane ne Ali Larijani?

Ali Larijani ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasar Iran, wanda aka san shi da matsakaicin ra’ayi da kuma ƙwarewa a harkokin gwamnati.

Sunansa Ali Ardeshir Larijani kuma an haife shi a shekarar 1958 a garin Najaf na ƙasar Iraƙi. Sunan mahaifinsa Ayatollah Hashem Amoli Larijani.

Ya fito daga babban gida daga iyali mai ƙarfi daga yankin Amol. Mujallar Time ta taɓa kwatanta danginsu da “Kennedys na Iran” saboda tasirinsu a siyasa.

Ya yi karatu a fannin lissafi da kimiyyar kwamfuta, sannan ya kammala digiri na uku a falsafar Yammacin Duniya, inda ya mayar da hankali kan falsafar Immanuel Kant.

Bayan juyin juya halin Musulunci na 1979, ya shiga rundunar juyin-juya hali ta IRGC sannan ya riƙe muƙamai daban-daban a gwamnati, ciki har da ministan al’adu da kuma shugaban gidan talabijin na ƙasa IRIB.

Ya kuma zama sakataren majalisar tsaron ƙasa da babban mai tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran a 2005, kafin daga bisani ya zama kakakin majalisar dokoki na tsawon wa’adi uku, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen amincewa da yarjejeniyar nukiliya ta 2015.

A watan Agustan 2025 ne ya koma matsayin sakataren majalisar tsaron ƙasa, inda ya sake zama ɗaya daga cikin jiga-jigan shugabannin Iran.

Me zai faru idan kisan Larijani ya tabbata?

Idan har Iran ta tabbatar da kisan Ali Larijani, hakan zai zama ɗaya daga cikin manyan kashe-kashen shugabanni mafi tasiri tun bayan fara yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar, wanda ya haɗa da harin da ya kashe marigayi jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei.

Bayan rasuwar Khamenei, an ce an naɗa ɗansa a matsayin sabon jagoran ƙasar, sai dai rahotannin Isra’ila na cewa sabon jagoran ya samu raunuka, kuma Larijani ne ke taka rawar jagoranci a matsayin babban jami’in tsaro.

Masana na ganin cewa kashe Larijani, idan ya tabbata, zai bai wa ƙasashen waje wahalar samun wanda za su tattauna da shi daga cikin manyan shugabannin Iran, musamman a wannan lokacin rikici.

Sai dai duk da haka, kisan nasa—ko da ya tabbata—ba yana nufin rugujewar tsarin mulkin Iran gaba ɗaya ba.

Tsarin mulkin ƙasar ya dogara ne da cibiyoyi da dama, ciki har da rundunar juyin-juya hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) da sauran hukumomin tsaro, waɗanda ke ci gaba da aiki duk da asarar manyan shugabanni.

A ɓangaren Isra’ila kuwa, za a ɗauki mutuwarsa a matsayin babbar nasara ta dabarun yaƙi, kasancewar zai rage ƙarfin jagoranci da haɗin kai a ɓangaren Iran.

Gani na ƙarshe da aka yi wa Larijani

A ranar Juma’ar da ta gabata an ga Larijani a bainar jama’a a yayin da yake halartar gangamin Ranar Qudus a tsakiyar Tehran.

Larijani ya kasance cikin manyan jami’an gwamnati da suka yi tattaki a gangamin na shekara-shekara, wanda ake gudanarwa domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

Bayyanar Larijani da shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian da ministan harkokin waje, Abbas Aragchi a jerin zanga-zangar sun musanta iƙrarin da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi cewa jagororin ƙasar Iran suna gudu su ɓuya saboda tsoron hare-haren.

Yayin da yake magana da kafafen yaɗa labaran gwamnati na Iran, ya bayyana harin bam da ya faru a lokacin gangamin a matsayin alamar “rauni da firgici” daga abokan gaban ƙasar.

“Waɗannan hare-haren sun fito ne daga matsorata masu rauni. Wanda yake da ƙarfi ba zai kai hari kan masu zanga-zanga ba. Saboda haka wannan a bayyane take sun gaza,” in ji shi.

Haka kuma ya soki shugaban Amurka, Donald Trump, yana mai cewa bai fahimci irin ƙarfin zuciya da jajircewar al’ummar Iran ba.

“Trump bai fahimci cewa mutanen Iran ƙasa ce mai jarumtaka da ƙarfi da jajircewa ba. Duk wani ƙarin matsin lamba, zai ƙara wa al’ummar Iran ƙarfin zuciya,” in ji Larijani.

Bayyanarsa a wannan gangami na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin iƙirarin da Isra’ila ta yi cewa an kashe shi.

Larijani ya nemi haɗin kan ƙasashen Musulmi a yaƙin Iran

A bayan nan kuma Ali Larijani, ya bayyana damuwa tare da aika saƙo mai ɗauke da gargaɗi da kuma kira ga ƙasashen Musulmi, yana mai jaddada cewa ƙasarsa ba za ta ja da baya ba a yaƙin da take yi da Amurka da Isra’ila.

A cikin saƙon da ya fitar, Larijani ya yi ƙoƙarin jan hankali ƙasashe da yawancinsu Musulmai ne, yana mai cewa, ban da kaɗan daga cikinsu, yawancin ƙasashen Musulmi sun gaza goyon bayan Iran kan abin da ya kira “muguwar hari na yaudara.”

Ya ambato maganar Annabi Muhammad (SAW) inda ya ce: “Duk wanda ya ji ana kiran ‘Ya Musulmi!’ bai amsa ba, to ba Musulmi ba ne,” yana mai tambayar ko matakin wasu gwamnatocin Musulmi bai saɓa da wannan koyarwa ba.

Larijani ya kuma kare hare-haren da Iran ke kaiwa a yankin, duk da cewa ƙasashen yankin Gulf na kallon hakan a matsayin keta huruminsu, inda ya nuna cewa babu tsaka-tsaki a wannan rikici.

“Wane ɓangare kuke?” in ji shi, yana mai aika wani saƙo na gargaɗi ga ƙasashen da ke ƙoƙarin kaucewa rikicin.

Sai dai ya jaddada cewa Iran ba ta neman mamaye maƙwabtan ta, yana mai cewa haɗin kan al’ummar Musulmi zai iya tabbatar da tsaro, ci gaba da ’yancin kai ga dukkan ƙasashe idan aka cimma shi yadda ya kamata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *