Sin Da Faransa Sun Yi Alkawarin Zurfafa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Hada-Hadar Kudi
[ad_1]
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng da ministan kudi na kasar Faransa Roland Lescure, sun yi shawarwari masu zurfi jiya Litini a birnin Paris, kan ci gaban da aka samu a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da hada-hadar kudi na Sin da Faransa da kuma sauran batutuwan da suka shafe su.
He, jagoran tawagar Sin ta tattaunawar tattalin arziki da hada-hadar kudi tsakanin Sin da Faransa a matakin koli, ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta hada kai da Faransa wajen aiwatar da matsayar da shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban Faransa Emmanuel Macron suka cimma. Ya kuma yi kira da a kara zurfafa mu’amala da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da hada-hadar kudi, da kuma karfafa dorewar ci gaban dangantakar tattalin arzikin kasashen biyu ba tare da tangarda ba.
Kazalika, He ya yi wa bangaren Faransa bayani kan tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sin da Amurka da aka gudanar a farkon wannan rana.
Shi ma da yake jawabi, jagoran tawagar tattaunawar ta Faransa Lescure ya bayyana cewa, kasar ta Faransa tana ba da fifiko sosai ga hadin gwiwa da kasar Sin, kuma tana son yin aiki tare da Sin wajen sa-kaimi ga yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da kudi, da kuma samun gagarumin ci gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link