CAF Ta Soke Nasarar Senegal, Ta Ayyaṇa Morocco A Matsayin Zakarar AFCON Ta 2025

[ad_1]

Babban kwamitin ɗaukaka ƙara na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), ya amince da ƙarar da ƙasar Morocco ta shigar, inda ya soke nasarar da tawagar Senegal ta samu a wasan ƙarshe na gasar AFCON ta 2025.

Kwamitin ya bayyana cewa, bayan duba ƙarar da aka shigar, an samu kura-kurai da laifuka daga ɓangaren Senegal a lokacin wasan na ƙarshe.

  • Tinubu Ya Bai Wa Masu Riƙe Da Muƙamai Da Ke Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-wadai Da Hare-haren Ƙunar Baƙin Wake A Maiduguri

Saboda haka, an yanke hukuncin bai wa Morocco nasara da ci 3-0, tare da ayyana su a matsayin zakarun gasar a hukumance.

Wannan hukunci ya soke na baya da kwamitin ladabtarwa na CAF ya yanke, bayan ƙungiyar kula da ƙwallon ƙafa ta Morocco (FRMF) ta ɗaukaka ƙara kan abubuwan da suka faru a wasan.

CAF ta bayyana cewa wasu halaye da ‘yan wasan Senegal suka nuna, ciki har da barin filin wasa da kuma jawo tsaiko na wasu mintuna, sun saɓa dokokinta, musamman sashe na 82 da 84 na dokokin gasar AFCON.

Saboda haka, hukuncin ƙarshe ya tabbatar da cewa Morocco ce ta lashe gasar AFCON a hukumance, bayan soke nasarar da Senegal ta yi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *