’Yan Bindiga Sun Sace Mutane Sama Da 20 A Katsina
[ad_1]
Aƙalla mutane sama da 20 ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar Litinin bayan sun kai hari ƙauyen Gidan Sarki da ke yankin Tuge a Ƙaramar Hukumar Musawa ta Jihar Katsina.
Wani masani kan tsaro mai suna Bakatsine ne ya bayyana hakan a shafinsa X a ranar Talata.
- Kasar Sin Ta Cimma Burinta Na Shekarar 2025 Da Mai Da Hankali Kan Kirkire-kirkire Da Bukatun Cikin Gida
- Kamfanonin Sin Masu Saurin Bunkasa Sun Kai Kaso Daya Bisa Uku Cikin Jimillar Makamantansu Na Duniya
A cewarsa, ’yan bindigar sun shiga ƙauyen, sun harbi wasu mutane, sun kwashe dabbobi, sannan suka sanya firgici a zukatan jama’a.
Wannan ya sa mutane da dama suka gudu suka bar gidajensu.
A halin yanzu, wasu suna kwana a dazuka, maƙabartu, rijiyoyin da aka daina amfani da su, saman rufin gidaje, da kuma ƙarƙashin bishiyoyi saboda tsoron kada ’yan bindigar su sake dawowa.
Bakatsine ya ce lamarin ya faru ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a baya tsakanin shugabannin ƙaramar hukumar da ’yan bindigar da ke yankin.
Ya ce ’yan bindigar sun kashe mutane, sun yi garkuwa da mutane sama da 20, sun sace dabbobi, lamarin da ya tilasta wa ɗaukacin al’ummar yankin tserewa.
Kawo yanzu, hukumomin tsaro da gwamnatin Jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da mazauna yankin ke ci gaba da tantance asarar da suka yi.
[ad_2]
Source link