Matasa A Jihar Nasarawa Sun Buƙaci Gwamnati Ta Inganta Wutar Lantarki
[ad_1]
A ranar Litinin da ta gabata ne, matasa suka fita kan titunan garin Lafia, Babban Birnin Jihar Nasarawa, suna neman a inganta musu wutar lantarki a faɗin jihar.
An ga mazauna garin ɗauke da alluna tare kuma da rera waƙoƙi, kan abin da suka bayyana a matsayin rashin samar da wutar lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja (AEDC) ya yi.
- Zan Tabbatar Duk Ƴan Dakon Hatsi A Nassarawa Sun Mallaki Katin Zaɓe — Alhaji Danji
- Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa
Har ila yau, sun zargi kamfanin rarraba wutar da “sanya su a duhu” duk da matsalolin da mazauna yankin suke fama da su.
Jagoran masu zanga-zangar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Attama, ya ce; babban birnin jihar, ya daɗe yana fama da matsalar rashin isasshiyar wutar lantarki, yana mai bayyana lamarin a matsayin wanda yake gurgunta tattalin arziƙi da walwalar al’umma.
Ya ƙara da cewa, daɗewar da aka yi ana fama da matsalar rashin tsaro da kuma gurgunta ƙananan sana’o’i, yana da alaƙa da wannan matsala.
“A duk al’ummar da babu haske a tare da ita, babu rayuwa mai daɗi, domin kuwa kasuwanci yana rushewa, rashin tsaro yana ƙaruwa, sannan kuma mazauna yankin suna fama da buƙatu iri daban-daban,” in ji shi.
Kwamared Atama ya lura cewa, duk da cewa; tana da muhimmanci da kuma tasiri ga tattalin arziƙin ƙasar, amma rabon wutar lantarkin ga jihar, ko kaɗan bai isa ba, musamman domin biyan buƙatun da ake da su, wanda hakan ke haifar da durƙusar da ƙananan sa’o’i da kuma rashin tabbas a tsakanin al’umma.
Har wa yau, Atama ya bayyana cewa; zanga-zangar na nufin jawo hankalin gwamnati, ba tayar da hayaniya ko tarzoma ba.
“A bayyane yake cewa, rabon wutar lantarki ga Jihar Nasarawa, musamman babban birnin jihar, ko kaɗan bai wadatar ba, musamman wajen biyan buƙatun da ake da su.
Sannan, ya buƙaci gwamnati da ta yi hulɗa da hukumomin samar da wutar lantarki ta tarayya, don tabbatar da samun isasshiyar wutar lantarkin da kuma samun daidaitaccen rabon wutar ga jihar.
[ad_2]
Source link