Sojoji sun ƙaryata rahoton kashe dakarunsu 40 a Borno
[ad_1]
Rundunar Sojin Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an kashe sojoji sama da 40 a hare-haren da Boko Haram ta kai a Jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar Operation HADIN KAI a Arewa Maso Gabas, Laftanar Kanal Sani Uba ne, ya bayyana hakan.
Ya ce rahoton da wata kafar sadarwa ta wallafa ya wuce gona da iri kuma ba a tabbatar da sahihancinsa ba, don haka ya buƙaci jama’a su yi watsi da shi.
“Rahoton da ke cewa an kashe sojoji sama da 40 a hare-haren ta’addanci da aka kai a Borno ba gaskiya ba ne, kuma ya dogara ne kan bayanai da ba a tabbatar da su ba,” in ji Uba.
Ya bayyana cewa hare-haren sun faru ne bayan ragowar mayaƙan Boko Haram da aka fatattaka daga dajin Sambisa suka sake haɗuwa suka kai hare-hare kan al’ummomi da sansanonin sojoji a yankunan Konduga, Ngoshe, Mainok da Jakana.
Ya ƙara da cewa sojojin da ke wajen sun yi gaggawar mayar da martani tare da kare al’ummomin da aka kai wa hari.
“Sojojinmu sun yi jarumtaka wajen daƙile harin ’yan ta’addan da kuma kare al’ummomin.
“An kashe wasu daga cikin ’yan ta’addan a yayin artabun, amma abin takaici wani kwamandan runduna da wasu sojoji sun rasa rayukansu,” in ji shi.
Rundunar sojin ta kuma ce ba a fatattaki sojojin ba kamar yadda rahoton ya nuna, domin sun fafata da maharan domin kare jama’ar yankin.
Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ziyarci sojojin da ke aiki a Maiduguri, inda ya ba da umarnin ƙara tura sojoji da kayan aiki domin ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda.
Rundunar sojin ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta ci gaba da kai farmaki har sai ta murƙushe dukkanin ƙungiyoyin ta’addanci.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link