’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi

[ad_1]



Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hakimin Bagaji Odo a Karamar Hukumar Omala ta Jihar Kogi, David Wada.

Rahotanni sun ce basaraken ya faɗa tarkon ’yan bindigar ne a ƙauyen Ojuwo Ugweche da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, yayin da yake dawowa daga taron sarakunan gargajiya a Abejukolo, hedikwatar ƙaramar hukumar.

Wani mazaunin yankin, Maji Ahiaba, ya bayyana cewa a ’yan kwanakin nan ƙauyen Ojuwo Ugweche na fuskantar hare-haren masu ta’adar garkuwa da mutane, duk da cewa a baya an taɓa tura jami’an tsaro da ’yan sa-kai domin daƙile ayyukan miyagun.

Sai dai a cewar mazaunin a wannan karo da abun ya faru, babu jami’in tsaro ko guda a yankin.

Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na ƙaramar hukumar, Sarkin Ife, Mai Martaba Boniface Musa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya roƙi jami’an tsaro su bi sahun masu garkuwar domin ceto basaraken da aka sace.

Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Kogi, SP Williams Aya, ya ce tuni an tura jami’an tsaro, mafarauta da kuma ’yan sa-kai domin su tsefe dajin da ake zargin an kai sarkin da zummar ceto shi cikin aminci.

Sai dai har yanzu iyalai da kuma al’ummar yankin na cikin fargaba, la’akari da cewa tun bayan sace basaraken babu wanda masu garkuwar suka tuntuɓa.

A bara ne wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a Bagana, Bagaji, Agojeju Odo da Ajokpachi Odo ya bai wa ’yan bindiga damar kashe ɗaruruwan mutane a yankin, lamarin da aka samu aminci bayan Gwamna Usman Ahmed Odo ya tura sojoji da jami’an tsaro.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *