Sojoji Sun Kama Mai Tsara Harin Ƙunar Baƙin Wake A Arewa-Maso-Gabas

[ad_1]

Dakarun Sojojin Nijeriya sun kama Sheriff Umar, wanda aka gano a matsayin babban mai tsara hare-haren ƙunar baƙin wake a Arewa-Maso-Gabas.

An kama shi ne bayan wani bincike da aka gudanar a Maiduguri a ranar 31 ga watan Disamba, 2025, inda sojoji suka kama wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a hare-haren ƙunar baƙin waken.

  • Sojoji Sun Nemi Ƴan Sokoto Su Miƙa Ragowar Ɓaraguzan Bam Ɗin Amurka
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kudiri Aniyar Bunkasa Sana’ar Kiwon Dabbobi Ta Mata —Minista

Binciken daga baya ya tabbatar cewa Sheriff Umar, wanda ake kira Yusuf, shi ne shugaban ƙungiyar.

Hukumomi sun ce shi ke da alhakin ɗaukar maharan ƙunar baƙin waken, shirya su, tura su zuwa wuraren da za su kai hari, da kuma samar da kayan fashewa.

An danganta shi da harin ƙunar baƙin waken  da aka kai Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga watan Disamba, 2025, da kuma harin da aka daƙile a Damaturu.

Bincike ya nuna cewa matarsa da ‘yar matarsa sun san abubuwan da ke faruwa.

Duk wanda ake zargi suna hannun jami’an tsaro yayin da ake ƙoƙarin daƙile ƙarfin ƙungiyar.

Sojoji sun yi kira ga jama’a da su ci gaba da lura da abubuwa a yankunansu, tare da bayar da rahoto ga jami’an tsaro, inda suka jaddada cewa haɗin kai tsakanin al’umma da sojoji shi ne mabuɗin kawo ƙarshen ta’addanci a yankin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *