Mutum 23 sun faɗa komar ’yan bindiga a ƙauyen Sakkwato
[ad_1]
Aƙalla mutum 23 ne suka faɗa komar ’yan bindiga a ƙauyen Gajit da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa maharan masu yawa sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 2:30 na dare a ranar Laraba.
Wani ɗan uwan wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su ya ce ’yan bindigar sun yi dabara wajen ruɗar mazauna ƙauyen kafin su kai harin.
“Mu kan yi aikin sintiri domin tabbatar da tsaro daga ƙarfe 10 na dare har zuwa 2 na dare, inda a wannan karon sai da suka bari mun kwanta barci sannan suka kawo harin,” in ji shi.
Ya bayyana cewa da farko mutane 28 aka sace, ciki har da mata da ’ya’yansu da kuma maza uku. Sai dai daga bisani suka saki mutum guda da ƙananan yara uku, wanda hakan ya sa adadin waɗanda ke hannun ’yan bindigar ya koma 23.
Majiyar ta kuma zargi jami’an tsaro da rashin ba da haɗin kai, inda ta ce duk kiran da aka yi na neman su kawo ɗauki a lokacin aukuwar harin bai haifar da ɗa mai ido ba.
“Mun yi ta kiran neman agaji amma babu wani jami’in tsaro da ya kawo mana ɗauki yayin aukuwar harin,” in ji shi.
Mazauna sun yi kira ga gwamnati da ta tura ƙarin jami’an tsaro yankin, suna cewa yanzu haka suna rayuwa cikin tsoro da fargaba.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato amma samun wayar kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link