Wani mutum ya kashe kansa saboda wahala da rashin kuɗi
[ad_1]
A safiyar ranar Juma’a ne aka samu wani mutum mai shekara 50 mai suna Odomma a unguwar Amakpu Okuku da ke Ƙaramar hukumar Owerri ta jihar Imo, inda aka tsinci gawarsa bayan anyi zargin ya kashe kansa.
Mazauna yankin sun ce, Odomma mahaifin ’ya’ya huɗu ne da ke sayar da ruwa a jarkoki da bokiti, ya daɗe yana kokawa da matsalar rashin kuɗi da ta sa ya kasa ciyar da kansa da iyalansa.
An gano gawarsa rataye ne a wani gini da ba a kammala ba a kusa da gidansa yayin da mutane ke kan hanyarsu ta yau da kullun.
A cewar mazauna ƙauyen, kimanin watanni uku da suka gabata Odomma ya yi barazanar kashe kansa, inda ya yi ƙorafin cewa matarsa da ’ya’yansa sun daina ba shi abinci saboda ya gaza ciyar da iyalinsa.
Wani ɗan unguwar mai suna Ikenna ya shaida wa majiyar Punch cewa marigayin ya bayyana takaicinsa da wasu abokansa.
“Ya ce idan lamarin ya ci gaba, zai iya ɗaukar ransa don ya kawo ƙarshen wannan rayuwar ƙunci.
“Mun shawarce shi da ya kai rahoto ga Dakacin Ƙauyen don sasantawa, abin baƙin ciki shi ne ya zaɓi wannan hanya, ka ga yadda mutumin nan ya kashe rayuwarsa saboda kuɗi, zai iya sayar da tankin ruwa GP ɗinsa ko janareta don ya samu abinci, amma ya yanke shawarar kashe kansa, yanzu wasu za su taru su cinye abin da ya mallaka kuma ba zai shiga ciki ba,” inji Ikenna.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link