Japan ta ware wa ’yan Najeriya birni don zama a ƙasar
Gwamnatin Ƙasar Japan ta ware birnin Kisarazu a matsayin garin ’yan Najeriya da ke son zama don yin aiki a ƙasar.
Wannan mataki na cikin shirin Japan na ƙarfafa alaƙar al’adu, bunƙasa tattalin arziƙi da kuma ƙara yawa ma’aikata a ƙasar.
Gwamnatin za ta ƙirƙiri sabuwar biza ta musamman domin ’yan Najeriya waɗanda ke son yin hijira zuwa Kisarazu.
Haka kuma, ’yan Najeriya masu sana’o’i da sauran ma’aikata da ke son inganta fasaha za su amfana da wannan biza.
Japan kuma haɗa wasu ƙasashen Afirka cikin wannan shiri.
An ware Nagai da ke lardin Yamagata a matsayin garin Tanzaniya, Sanjo da ke lardin Niigata a matsayin garin Ghana, sannan Imabari da ke lardin Ehime a matsayin garin Mozambique.
Jakadiyar Najeriya a Japan, Florence Akinyemi Adeseke, tare da magajin garin Kisarazu, Yoshikuni Watanabe, sun karɓi takardar shaidar tabbatar da wannan gari.
An yi tsammanin wannan shiri da zai ƙarfafa alaƙa tsakanin Japan da waɗannan ƙasashen Afirka, tare da taimaka wa biranen Japan wajen farfaɗo da tattalin arziƙin yankunan.
Garin Kisarazu yana alaƙa da ‘yan Najeriya, domin a nan ne aka karɓi tawagar ’yan wasan Najeriya a lokacin ɗaukar horo kafin gasar Olympics ta Tokyo 2020.
A lokacin taron ci gaban Afirka na Tokyo (TICAD), Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya bayyana sanya hannun jarin dala biliyan 5.5 da za su yi a Afirka.
Ya jaddada muhimmancin haɓaka tattalin arziƙi da ’yan kasuwa ke jagoranta, tallafa wa matasa da mata, da kuma haɗin kan ƙasashe.
Ya kuma bayyana ƙalubalen da Japan ke fuskanta, kamar ƙarancin gonaki, tare da neman haɗin gwiwar ƙasashen Afirka wajen nemo mafita game da matsalar.