Ƴansanda Sun Cafke Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Kisan Wata Lauya A Abuja
[ad_1]
Rundunar ƴansandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta kama mutum uku da ake zargi da hannu a kisan wata lauya, Chigbo Princess, da kuma ayyukan fashin makami na “one-chance” a Abuja.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta fitar a ranar Lahadi.
Adeh ta bayyana cewa kamen ya biyo bayan umarnin Kwamishinan Ƴansanda na FCT, Miller Dantawaye, na gano tare da cafke dukkan mutumn da ke da alaƙa da laifin.
Ta ce jami’an rundunar daga Scorpion Sƙuad, ƙarƙashin jagorancin ACP Ɓictor Ogbeide Godfrey, sun bibiyi wayar salular mamaciyar ta hanyar amfani da bayanan sirri na zamani, inda suka gudanar da ayyuka tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga Janairu a yankunan Dei-Dei, Dakwa da Dan-Tata da ke Kubwa.
- Sojoji Sun Daƙile Harin Fashi Da Makami A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
- Shirin Sauya Sheƙa: An Tsaurara Tsaro A Harabar Gidan Gwamnatin Kano
Wani sashen sanarwar ya ce: “Rundunar ƴansandan FCT ta samu gagarumar nasara a yaƙi da laifuka masu tsanani, bayan kama wasu fitattun ƴan fashi da makami uku da ke da hannu a ayyukan ‘One-chance’ da kuma mummunan kisa kan wata lauya, Chigbo Princess.
“Tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga Janairu, 2026, jami’an Scorpion Sƙuad na rundunar, karkashin jagorancin ACP Ɓictor Ogbeide Godfrey, bisa bayanan sirri na zamani da aka sake gina su, sun bibiyi wayar salular mamaciyar tare da gudanar da ayyukan bin diddigi a al’ummomin Dei-Dei, Dakwa da Dan-Tata da ke yankin Kubwa na FCT.
“Waɗannan ayyuka na dogaro da bayanan sirri sun kai ga kama waɗannan mutum: Saifullahi Yusuf (namiji, mai shekaru 22) – daga Ƙaramar Hukumar Kaduna North a Jihar Kaduna, mazaunin yankin Dan-Tata, Dei-Dei, Abuja.”
“Ishau Yusuf mai shekaru 24 daga Samaru, Zariya, Jihar Kaduna, mazaunin yankin Dan-Tata, Dei-Dei, Abuja.
Minka’ilu Jibril, wanda aka fi sani da Dan-Hajia, shi ma daga Ƙaramar Hukumar Kaduna North a Jihar Kaduna yake.
“Ya dace a lura cewa wanda ake zargi na farko da na biyu ƴan uwa ne na jini. Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin mambobin wata fitacciyar ƙungiyar fashi da makami ta ‘one-chance’ ne, wadda ta shafe shekaru tana aikata laifuka lokaci zuwa lokaci a cikin FCT, musamman a lokutan bukukuwa.”
Adeh ta ce bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun yi wa mamaciyar barazana, suka buƙaci kuɗi, sannan daga bisani suka turo ta daga cikin motar da ke tafiya, abin da ya janyo mutuwarta.
“Bincike ya ƙara gano cewa a ranar 5 ga Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 5:50 na yamma, Barrista Princess Chigbo ba tare da sani ba ta shiga wata baƙar mota kirar Ɓolkswagen Golf 3 a kan titin Kubwa Eɗpressway, ba tare da sanin cewa mutumn da ke cikin motar ƴan ta’adda ba ne.
“Da ta shiga motar, waɗanda ake zargin suka daga gilashin motar mai duhu, suka yi mata barazana da makamai domin tilasta mata biyan kuɗin fansa domin a sake ta.
“Lokacin da ta ƙi ba da haɗin kai, an doke ta sannan aka turo ta daga cikin motar da ke tafiya a kan titin Kubwa Motorway, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta,” in ji ta.
Adeh ta ce wadanda ake zargin sun ƙwace wayar salular Android ta mamaciyar tare da sayar da ita a Dei-Dei kan kuɗi Naira 120,000.
“Waɗanda ake zargin sun kuma amsa cewa sun ƙwace wayar Android ta mamaciyar, wadda daga bisani aka sayar a Dei-Dei kan Naira 120,000.
“Daga cikin kuɗin, Minka’ilu Jibril ya karɓi Naira 30,000, Saifullahi Yusuf ya karɓi Naira 15,000, yayin da Ishau Yusuf da wani wanda ake zargi da ya tsere a halin yanzu mai suna Musa suka raba sauran kuɗin,” in ji Adeh.
Adeh ta ƙara da cewa kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da almakashi guda biyar, wuƙaƙe masu kaifi biyu, doguwar sarka ɗaya da kuma wani kayan kama hannu (plier).
Jaridar The PUNCH ta ruwaito a baya cewa an tsinci gawar Ochigbo a kan titin Kubwa Eɗpressway a ranar Talata, tare da jakarta da ke ɗauke da katin shaida da wasu kayanta, wanda aka same su a ƴan mitoci kaɗan daga inda aka tsinci gawar.
Takardun da aka samu daga mamaciyar sun nuna cewa wata kila ma’aikaciya ce a Kotun Ƙoli ta FCT.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Adeh ta tabbatar da cewa jami’an bincike sun fara aiki kan lamarin.
Wannan lamari ya zo ne jim kaɗan bayan kisan wata Nas mai suna Chinemerem Chuwumeziem a Asibitin Ƙasa na Tarayya (FMC), Jabi.
Mutuwarta ta janyo fushin jama’a da kuma Allah-wadai daga Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Nijeriya (NANNM), reshen FCT.
[ad_2]
Source link