Sin Da Canada Sun Cimma Matsayar Shawo Kan Sabanin Cinikayya A Tsakaninsu
[ad_1]
Kasashen Sin da Canada, sun aiwatar da wasu shirye-shirye dake da nufin shawo kan sabanin cinikayya a tsakaninsu, a bangarori masu alaka da motoci masu amfani da lantarki da kayayyakin karafa da goran ruwa da kayayyakin gona da na ruwa.
Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ce ta bayyana haka a jiya Jumma’a, inda ta ce domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, bangarorin biyu sun gudanar da tattaunawa da dama tare da tuntubar juna a matakai daban-daban, inda suka mayar da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya da suka shafe su.
Har ila yau, bangarorin biyu sun cimma matsayar kara yawan zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu da inganta muhallin kasuwanci da kuma tantance ingancin amfanin gona.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta ce wannan wani mataki ne mai muhimmanci wajen warware sabanin cinikayya a tsakaninsu dake alamta wani sabon mafari na zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.
A cewar sanarwar, bangarorin biyu za su yi cikakken amfani da tsarin kwamitin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na Sin da Canada wajen ci gaba da fadada hadin gwiwarsu da warware sabani da hakuri da bambance-bambance da daukaka dangantakar tattalin arziki da cinikayya mai aminci da karko da dorewa a tsakaninsu. (FMM)
[ad_2]
Source link